Gombe za ta samar da sabon irin masara ga manoman rani
Gwamnatin Jihar Gombe ta shirya samar wa manoman rani irin masara mai inganci da ya kai Naira miliyan 20 domin karfafa noman rani a jihar. Kwamishinan Gona da Dabbobi na Jihar, Alhaji Muhammadu Magaji Gettado ne ya bayyana haka lokacin da yake zantawa da wakilinmu, a yayin taron manoman rani na shinkafa da Babban Bankin […]
Gwamnatin Jihar Gombe ta shirya samar wa manoman rani irin masara mai inganci da ya kai Naira miliyan 20 domin karfafa noman rani a jihar.
Kwamishinan Gona da Dabbobi na Jihar, Alhaji Muhammadu Magaji Gettado ne ya bayyana haka lokacin da yake zantawa da wakilinmu, a yayin taron manoman rani na shinkafa da Babban Bankin Najeriya (CBN) da Bankin Unity da Hukumar Inshorar Noma ta Kasa (NAIC).
Ya ce ma’aikatar ta zakulo manoman masara fiye da dubu daya domin cin gajiyar shirin.
Ya ce wannan tsari na Ma’aikatar Gona ya sha bamban da sauran tsare-tsare domin ba kayayyakin da za su bayar bashi ba ne za su sayar wa manoma ne a kan farashi mai sauki; inda manomi zai biya nan take ya dauka.
Gettado, ya ce irin masarar kyauta ce, domin a gwada shi a gani kuma manoman rani za a bai wa. Ya hore su da kada su ajiye sai lokacin damina; su noma yanzu don ana so a gwada ingancinsa ne a gani kafin lokacin noman damina ya yi.
Kwamishinan ya ce Gwamnan Jihar Gombe Alhaji Inuwa Yahaya ya kawo irin ne domin a taimaka wa manoma da makiyaya a jihar da nufin wadata kasa da abinci.
Sai ya yi kira ga shugabannin cewa duk kayayyakin da aka kayyade domin manoma a ba su kada a ce a bai wa manomi taki buhu 10 wani ya rage ya ba shi biyar ko bakwai.
Ga manoman shinkafar da shirin Anchor Borrowers zai bai wa rancen noma kuwa ya ce domin gudun kada a cuce su kamar yadda ya faru a baya shi ne yanzu ake zama da su ana sanar da su farashin kayayyakin da sai sun yarda kafin a amince a kawo musu.
Alhaji Magaji Gettado, ya ce idan aka gama zama aka amince za a bai wa kowane manomi kaya da kudi a kan lokaci. Idan kuma aka zo karshe aka ga idan an bai wa manoman kayan za su cutu to za su dakatar.
Daga nan sai ya ce duk manomin da aka bai wa kaya idan ya girbe amfanin gonarsa ba da kudi zai biya ba da amfanin da ya noma irin wanda aka ba shi zai biya.