Gomman ’yan Boko Haram sun miƙa wuya a yankin Tafkin Chadi
Matansu ma ana ɗaukarsu a matsayin ’yan ta’adda, saboda ana amfani da su a kai harin ƙunar-baƙin-wake.
Rundunar haɗaka da ke aikin wanzar da tsaro a yankin Tafkin Chadi ta ce mayaƙan Boko Haram da dama sun miƙa wuya a watan Yuli ga dakarun rundunar a Nijar da Kamaru.
Waɗanda suka miƙa wuyan “maza 14 ne da mata 23 da yara 32,” kamar yadda Laftanal Kanal Abubakar Abdullahi, mai magana da yawun rundunar ya bayyana ranar Talata.
- Kawu Sumaila ya miƙa ƙudirin ƙirƙiro sabuwar jiha daga Kano
- Ganduje da matarsa za su bayyana a kotu kan zargin almundahana
“Matansu ma ana ɗaukarsu a matsayin ’yan ta’adda, saboda ana amfani da su a kai harin ƙunar-baƙin-wake,”
“Kuma suna miƙa wuya ne sakamakon toshe duk wata hanya da suke samun kayayyakin masarufi,” kamar yadda ya bayyana.
An kafa Rundunar Dakarun ta Haɗaka ce a 1994 don daƙile laifukan da ake aikatawa tsakanin ƙasashen, sai dai an ɗora mata nauyin faɗaɗa ayyukanta zuwa yaƙi da Boko Haram, wacce ’yan ƙungiyar ke kai hare-hare a ƙasashe maƙwabta daga cibiyarta a Nijeriya.
Wani ɗan Boko Haram wanda ya tsere daga sansanin Libye Soroa a Nijar ya miƙa wuya ga rundunar ranar 1 ga watan Yuli, sannan ya miƙa “bindiga ƙirar AK-47, da magazin guda hudu, da albarusai da dama” a cewar rundunar a cikin wata sanarwa.
Wasu mutanen kuma 56 da suka haɗa da maza 13 – da rakiyar matansu da ’ya’yansu – sun miƙa wuya, bayan wani aikin haɗin gwiwa na sojojin ruwan Nijeriya da Kamaru” a ranar 6 ga Yuli, a ɓangaren arewa mai nisa ta Kamaru, kamar yadda sanarwar ta bayyana.
A wannan ranar ne kuma, “aka kuɓutar da iyalan ’yan ta’addar 12,” — mata biyar da yara bakwai — a cewar sanarwar.
Rundunar da ta haɗa dakarun Nijeriya da Nijar da Kamaru da Chadi ta kuma yi kira ga mayaƙan Boko Haram su “ajiye makamansu su kuma miƙa wuya ga hukumomi don samar da zaman lafiya mai ɗorewa a yankin Tafkin Chadi.”