Goodluck da Babangida sun gana cikin sirri a Minna
Tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathen ya kai wa tsohon shugaban qasa na mulkin soji, Ibrahim Badamasi Babangida ziyara a gidansa da ke Minna. Jonathan wanda ya shigo a bakar mota kirar SUV mai sulke mai lamba ABJ 961ER tare da rakiyar motoci 8, ya isa gidan Babangida da misalin karfe 10 na safe. Sannan sun […]

Tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathen ya kai wa tsohon shugaban qasa na mulkin soji, Ibrahim Badamasi Babangida ziyara a gidansa da ke Minna.
Jonathan wanda ya shigo a bakar mota kirar SUV mai sulke mai lamba ABJ 961ER tare da rakiyar motoci 8, ya isa gidan Babangida da misalin karfe 10 na safe. Sannan sun tattauna cikin sirri har zuwa misalin karfe 12 da minti 14.
Bayan ya fito, tsohon shugaban qasar, Jonathan ya ki yin bayanin dalilin ziyarar, inda ya ce “Tsakanin su ne kawai”
Da aka matsa masa, sai ya ce ya zo ne kawai domin ya gaishe da Babangida.
“Tun da Janaral Babangida ya dawo daga jinya, ban zo na gaishe shi ba. Shi yasa na zo yau domin na duba shi,” inji Jonathan.
Da aka tambayeshi a kan yanayin da kasa ke ciki a yanzu, sai ya ce “Ni yanzu ai na bar siyasa. Amma ‘yan jarida, kuna aiki kokari sosai.”