Google ya horar da ma’aikatan NOUN dabarun kasuwancin zamani
Manyan ma’aikatan Jami’ar NOUN a Kaduna sun halarci wani taron horo a kan dabarun kasuwancin zamani wanda Google ta shirya. Taron, wanda ya gudana a Cibiyar Cigaban Al’umma ta jami’ar (CHRD) ya qunshi ma’aikatan cibiyar, ma’aikatan jami’ar na Kaduna da kuma ma’aikatan jami’ar na barikin sojan saman Najeriya. Mista Leslie Babangida Dongh, wanda shi ne […]
Manyan ma’aikatan Jami’ar NOUN a Kaduna sun halarci wani taron horo a kan dabarun kasuwancin zamani wanda Google ta shirya.
Taron, wanda ya gudana a Cibiyar Cigaban Al’umma ta jami’ar (CHRD) ya qunshi ma’aikatan cibiyar, ma’aikatan jami’ar na Kaduna da kuma ma’aikatan jami’ar na barikin sojan saman Najeriya.
Mista Leslie Babangida Dongh, wanda shi ne jami’in bayar da horo daga Coverage Media wanda ke xaya cikin kamfanonin da Google ta zava guda shida domin bayar da horon ya ce “A shekarar 2016, Google ta yi shirin horar da ’yan Najeriya guda miliyan 1 da kuma ’yan yankin Afirka baki xaya a kan ci gaban zamani.”
Maqasudin bayar da horon, kamar yadda Google ta sanar, shi ne a koyar da mutane yadda za su yi amfani da yanar gizo yadda ya kamata ta hanyar qara shigar su, hakan zai taimaka wajen cin moriyar yanar gizon sosai ta hanyar samun dama masu yawa.
A wajen taron, an gabatar da maqala guda 3: “Yadda ake samun dama a yanar gizo”, “Yadda ake qara yaxuwa a yanar gizo”, “Samun aiki a kasuwancin zamani,” waxanda dukkansu Mista Leslie Babangida Dongh ne ya gabatar.