Gorge de Kola: Duwatsun masu launi daban-daban

Wani wurin yawon bude ido da yake garin Guider na yankinn Arewacin kasar Kamaru wani waje ne da ke kayatar da duk wanda ya ziyarce shi.Sunan wurin Gorge de Kola  kuma ya samo asali ne daga duwatsun da wannan wuri na garin Kola yake amansu. Akasarin mazauna garin Kola dai manoma ne da kuma makiyaya. A […]

Gorge de Kola: Duwatsun masu launi daban-daban
Gorge de Kola: Duwatsun masu launi daban-daban

Wani wurin yawon bude ido da yake garin Guider na yankinn Arewacin kasar Kamaru wani waje ne da ke kayatar da duk wanda ya ziyarce shi.
Sunan wurin Gorge de Kola  kuma ya samo asali ne daga duwatsun da wannan wuri na garin Kola yake amansu.
 Akasarin mazauna garin Kola dai manoma ne da kuma makiyaya. A lokacin damina ruwa na shayar da ’yan kogunan da garin ya kunsa, a yayin da kuma idan lokacin  rani ne sai duka su kafe.
Idan hakan ya faru ana barin awakai da raguna, tunkiya da kuma jakuna da jama’a suke kiwo su watsu cikin gari suna neman ruwan jika makogwaronsu. Sai dai baya ga wannan matsalar kasancewa garin da yake yankin Sahel mai fuskantar karancin ruwa, Allah Ya yi wa garin Kola wata kyauta ta musamman da take janyo mata jama’a da dama masamman ma masu yawon bude ido daga ciki da kuma wajen Kamaru.
 Wannan kyautar ita ce wasu salon duwatsu da suke tsage suka fidda launin ababe daban-daban wadanda idanun wanda ya kai ziyara wannan wurin zai shaida.
Ana kiyasta fadin filin da duwatsun suka shumfudu a kai a kan Kadada uku masu nauyin  dubannin tan na duwatsu masu kaloli daban-daban. Sai dai duk wani wanda zai kai ziyara wannan wurin ya kamata ya samu dan rakiya da zai  raka shi s sako da lungun wannan wuri.
Hari la yau, sai an gabatar da shi ga Basaraken garin kafin ya karasa wurin. Sarkin yana dauke da tarin wasu kayayyakin tarihin. Idan mutum  ya yi sa’a zai ba ka labarin wasu dakuna mallakin aljanu a cikin wadannnan kogon duwatsu. Sai dai ba za a iya tabbatar da hakan ba.
Hakazalika, kifaye na bullowa  cikin ruwan da wadannan duwatsu suka kunsa so daya a shekara. Wannan yana bai wa al’umar wannan garin  damar kamun kifi har na tsawon kusan wata guda. Daga bisani kuma sai kifayen su kare, sai badi.
Bugu da kari, yakamata duk wani wanda yake so ya ziyarci “Gorge de Kola” ya yi hakan tsakanin watannin Disamba zuwa watan Mayu wato lokacin kaka ke nan. A lokacin damina daukacin duwatsun na sulmuye a cikin ruwa. Sa’annan yakamata da mutum ya tanadi takalmi mai inganci a kafarsa wanda zai jure wa zafin rana, saboda wasu duwatsu na daukan zafin rana matuka.