Griezmann ya yi ritaya daga buga wa Faransa ƙwallo

Ɗan wasan mai shekaru 33 a duniya, ya bayyana hakan ne a shafinsa na X.

Griezmann ya yi ritaya daga buga wa Faransa ƙwallo

Ɗan wasan gaba na ƙasar Faransa, Antoine Griezmann, ya yi ritaya daga murza wa ƙasarsa leda.

Ɗan wasan mai shekaru 33 a duniya, ya bayyana haka ne a ranar Litinin.

Griezmann ya shafe shekaru 10 yana buga wa Faransa ƙwallo, inda ya buga wasanni 137.

“Zuciya cike da ɗimuwa nake sanar da rufe babin rayuwata da Faransa,” kamar yadda ya wallafa a shafin X (Twitter).

Ɗan wasan gaban na Atletico Madrid, ya fara buga wa Faransa wasa a watan Maris ɗin 2014, inda ya buga wasanni 14 tare da jefa ƙwallaye 44.

Griezmann shi ne ɗan wasa na huɗu daga cikin ’yan wasan da suka fi jefa wa Faransa ƙwallo a raga, inda yake bin bayan Olivier Giroud, Thierry Henry da kuma kyaftin ɗin tawagar Kylian Mbappe.

Ɗan shekara 60 ya rasu a hatsarin kwalekwale a Sakkwato

Yadda gobara ta ƙone kasuwar babura a Zamfara

Mun fara binciken turmutsutsin tallafin abinci — Shugaban ’Yan Sanda

Tinubu ya soke ayyukansa saboda rasuwar mutane a Abuja da Anambra