Gubar harsashi ta jikkata mutane dama a Zamfara

Hotuna da wakilinmu na naɗa sun hasko mutane da dama sun ƙone a ƙafafu da cinya har zuwa mazaunai.

Gubar harsashi ta jikkata mutane dama a Zamfara

’Yan kasuwa da abokan hulɗa da dama sun jikkata yayin da gubar harsashi ta tarwatse wannan Talatar a Jihar Zamfara.

Aminiya ta ruwaito cewa, lamarin ya faru ne a babbar kasuwar garin Talatan Mafara wadda ke ci duk ranar Talata.

Galibi waɗanda lamarin ya rutsa da su ’yan kasuwar ne da kuma wasu abokan hulɗarsu da suka samu ƙonuwa da raunika daban-daban.

Hotuna da wakilinmu na naɗa ya hasko waɗanda lamarin ya shafa suna kwance ana kawo musu agaji, inda galibi sun ƙone a fuska da ciki da ƙafafu da cinya har zuwa mazaunai.