Gudaji Kazaure ya kifa a yunkurinsa na komawa Majalisa a 2023
’Yan Majalisar Tarayya masu ci sun kwashi kashinsu a hannu a zaben fitar da dan takarar APC a Jihar Jigawa.
’Yan Majalisar Wakilai masu ci akalla hudu cikin 11 daga Jihar Jigawa sun ci kasa a yunkurinsu na neman tikitin komawa kujerarsu a zaben 2023 a jam’iyyar APC.
Daga cikin wadanda suka sha kaye a zaben fitar da takarar majalisar wakilan har da dan ga-ni-kashe-nin Shugaba Buhar, Honarabul Muhammad Gudaji Kazaure , mai wakiltar Kazaure/Yankwashi/Gwiwa/Roni.
Shida daga cikin ’yan majalisar sun tsallake siradi da zaben fitar da ’yan takarar jam’iyyar da aka gudanar ranar Juma’a, a yayin da ragowar dayan kuma aka bayyana sakamakon nasa a matsayin wanda bai kammala ba.
Saurwan wadanda suka sha kasa su ne Hon. Yusuf Shitu Shitu Galambi mai wakiltar Gwaram wanda sah Idris ya kayar, Ado Sani Kiri mai wakiltar Ringim/Taura ya sha kaye a hannun Sa’ad Wada Taura.
Muhammad Musa Fagen Gawo mai wakiltar Babura/Garki Federal kuma ya sha kaye a hannun Aminu Kanta Babura.
Shi kuma mai wakiltar Birnin Kudu/Buji Magaji Da’u Aliyu da wasu mutum hudu suka lashe zaben fitar da dan takarar.
Aliyu wanda shi ne shugaban kwamitin majalisar kan wutar lantarki ya lashe zaben da kuri’a 87 inda ya kayar da abokin karawarsa, Hon Nasidi Ali mai kuria’ 17.
Sauran ‘yan Majalisar Tarayya da suka samu tikitin APC su ne Makki Abubakar Yenleman (Malam Madori/Kaugama); Ibrahim Abdullahi Kemba (Dutse/Kiyawa); Nazifi Sani Gumel (Gumel/ Maigatari/Gagarawa/Sule Tankarkar).
Sai kuma Yusuf Sa’idu Miga (Jahun/Miga) da kuma Abubakar Hassan Fulata
(Birniwa/Guri/ Kiri).
Zaben yankin (Hadejia/Auyo/Kafin Hausa) shi ne wanda bai kammalu ba.