Gudummawar dangin ma’aurata wajen mutuwar aure a kasar Hausa

Ko shakka babu aure wani halattaccen ginshiki ne na zamantakewa a tsakanin namiji da mace domin kariya daga fasadi, barna da kuma sharrin luwadi da sauran laifuka. Duka, a addinance da kuma al’ada, namaji ne ke zuwa ya nemi mace da aure ta hannun iyayensa daga iyayenta. Ko shakka babu yawan mutuwar aure a kasar […]

Gudummawar dangin ma’aurata wajen mutuwar aure a kasar Hausa
Gudummawar dangin ma’aurata wajen mutuwar aure a kasar Hausa

Ko shakka babu aure wani halattaccen ginshiki ne na zamantakewa a tsakanin namiji da mace domin kariya daga fasadi, barna da kuma sharrin luwadi da sauran laifuka. Duka, a addinance da kuma al’ada, namaji ne ke zuwa ya nemi mace da aure ta hannun iyayensa daga iyayenta.

Ko shakka babu yawan mutuwar aure a kasar Hausa abin takaici ne. Wasu na alakanta yawan mutuwar auren a kan ma’auratan. Wasu su zargi talauci, wasu kuma su ce zamani ne, wasu kuma su ce son zuciya ne da sauransu. Ko shakka babu wadannan abubuwan da na lissafa suna ba da ta su gudummowar wajen mutuwar aure a duniya ba ma a kasar Hausa ba kadai.
Wani abu da ake yawan fada daga cikin jerin abubuwan da ke yawan kashe aure a kasar Hausa shi ne “Dangin ma’aurata”. Dangin ma’aurata ko shakka babu suna kawo mutuwar aure da yawa a kasar Hausa. Wannan yana da nasaba ne da irin gutsiri-tsomar da suke yi a cikin aure. Hausawa na cewa” kwarya ta bi kwarya in ta bi akushi ba za ta moru ba”. Sau da yawa tun kafin a daura aure dangin ma’aurata ke lalata shi. Misali, tun lokacin da yaro ko yarinya ta/ya fitar da wanda yake/take so za ka ji dangi suna cewa wannan ba ta yi ba, ko kuma bai yi ba. Sai su ce matsiyaci ne, ko kuma yaro ne. Ko kuma a ce ’yar gidan wane ai matsiyata ne. ko kuma tun daga wajen lefen yarinya za ka ji danginta na cewa wannan lefen bai yi ba. Ko kuma danginsa su ce an tsawwala wa yaro. Haka zalika duk sauran abubuwan da ake yi na shirin biki sai a ce ba su yi ba. Hakan na sanya ma’auratan su ji babu dadi. Kuma mahaifan ma’auratan sukan taimaka wajen bata aure musamman mahaifiya mace sai ta ce yarinya ba ta yi ba, kamar ita za ta zauna da ita. To, daga baya idan an yi auren, sai ta yi ta cewa “Ni dai ba haka na so ba ,ko kuma ba da
yawuna ba”. Sai ta dawo ta ce yarinyar ba ta girmama ta. Kai haka dai za a yi ta kai ruwa rana har sai auren ya mutu.
Haka zalika kanne da yayye. Idan mata ne sai suce duk abin da aka saya wa matar gida su ma sai an saya masu. idan ba a saya masu ba su ce ta hana. Idan suka zo gidan dan uwansu su ce “Matarsa ta mallake shi” Idan kuma maza ne sai su yi ta shiga gidan kamar wani shago. Su ci
abinci su bar kwanon a nan. Idan ta yi magana su nemi su zage ta.Idan kuma ta gaya wa mijinta ya yi masu magana,sai su tafi gida su gaya wa Hajiya, ta hau bala’i. Ta ce ya fi son matar sa a kan ’yan’uwansa.
Idan kuma ’yan’uwanta ne su ce mijinta ba ya alheri. Idan kannenta maza suka zo kila tare da abokan wasanta (taubashi) ya hana su shiga, sai a ce yana neman raba zumunci, kai haka dai matsaloli iri-iri.
Duk irin wannan abubuwan ne da ke faruwa ya sanya Hausawa su ka zama kabila mai yawan mutuwar aure bayan Indiyawa a duniya. Ya zama wajibi ga dangin ma’aurata da su guji gutsiri-tsoma a cikin abin da bai kai ya kawo ba a cikin auren ’yan’uwansu, hakan ne zai kara masu mutunci da kima a wajen ma’auratan.
kwamared Abdulbaki Aliyu Jari katsina Lay-out Katsina +2348035424321