Gudun hijirar zabe: ’Yan Arewa da suka kaurace wa Kudu sun dawo
Wasu ’yan ci-rani daga Arewa, mazauna Jihar Kurosriba da a kwanan baya suka rika tururuwa suna tafiya garuruwansu na asali a loacin zabe, sun fara dawowa jihohin na Kudancin Najeriya. A kwanakin baya dai lamarin kaurar tasu ta jawo kamfar harkokin kasuwanci. ’Yan Arewar da ke gudanar da kananan sana’o’i kama daga wanke takalma zuwa […]
Wasu ’yan ci-rani daga Arewa, mazauna Jihar Kurosriba da a kwanan baya suka rika tururuwa suna tafiya garuruwansu na asali a loacin zabe, sun fara dawowa jihohin na Kudancin Najeriya. A kwanakin baya dai lamarin kaurar tasu ta jawo kamfar harkokin kasuwanci.
’Yan Arewar da ke gudanar da kananan sana’o’i kama daga wanke takalma zuwa yankan farce da kuma sana’ar tela sun dawo.
Tun farko an rika ba za jita-jitar cewa barazanar tashin hankali da tsagerun yankin Neja-Delta suka yi na cewa matukar dan yankinsu ya fadi zabe, za su tayar da kayar baya, dalili ke nan ya sanya aka ce wasu suka tsorata, suka shiga taitayinsu, suka yi ta kwashe iyalansu suna tafiya gida Arewa.
Binciken da Aminiya ta yi a Unguwar Hausawa da aka fi sani da suna Layin Bagobiri Kalaba, ta ga ’yan Arewa sun dawo suna ci gaba da harkokinsu kamar yadda suka saba.
Wakilinmu ya tambayi Abdullahi Nuhu Auduwa, ko yaya yake kallon sunan da ake kiran su da shi na ’yan gudun hijira ko gudun zabe; sai ya ce: “Mu ba gudun zabe muka yi ba, yawancinmu rajistar katin zabe da muka yi a Arewa ce muka yi, shi ya sa muka ga ya fi dacewa mu tafi can tun da babu yadda za a yi a ce mutum nada rajistar Jihar Bauchi, ya tsaya yin zabe a Kurosriba; domin na’urar tantace mai zabe za ta nuna cewa wannan kati ba na nan ba ne,” inji shi.
Shi ma da yake tofa albarkacin bakinsa, Alaramma Malam Goni, wani malamin addini a Kurosriba, ya bukaci ’yan Najeriya su dage da yi wa Shugaban kasa mai jiran gado addu’a ta alheri, shi kuma ya kamanta adalci da tafiya da kowa da kowa, wadanda suka zabe shi da ma wadanda yake ji ba su zabe shi ba, domin yanzu ya zama baban kowa a kasar nan.
Ya zuwa rubuta rahoton nan dai, harkokin kasuwanci sun ci gaba da kankama ba tare da nuna wa ’yan Arewa kyara kamar da can ba.