Gudun rikici ya sa na bar Kano – Sanusi Ado Bayero

Ciroman Kano kuma babban dan marigayi sarkin Kano, Alhaji Sanusi Ado Bayero ya bayyana cewa saboda gudun tashin hankali ne ya sanya ya fice daga  Kano bayan an zabi sabon sarki Malam Sanusi Lamido Sanusi.Sanusi Ado, wanda shi ne Hakimin Gwale, yana daga cikin mutane ukun da masu zaben sarki a masarautar Kano suka mika […]

Gudun rikici ya sa na bar Kano – Sanusi Ado Bayero
Gudun rikici ya sa na bar Kano – Sanusi Ado Bayero

Ciroman Kano, Alhaji Sanusi Ado BayeroCiroman Kano kuma babban dan marigayi sarkin Kano, Alhaji Sanusi Ado Bayero ya bayyana cewa saboda gudun tashin hankali ne ya sanya ya fice daga  Kano bayan an zabi sabon sarki Malam Sanusi Lamido Sanusi.
Sanusi Ado, wanda shi ne Hakimin Gwale, yana daga cikin mutane ukun da masu zaben sarki a masarautar Kano suka mika wa Gwaman Kano, Injiniya Rabi’u Musa Kwankwaso da wadansu mutane suke ganin shi ya kamata ya gaji mahaifinsa, ya bayyana wa wakilanmu ta waya cewa ba ya bar Kano ba ne saboda rashin lafiya, kamar yadda wadansu jaridu suka ruwaita.
Ciroman na Kano ya bayyana cewa, “Don Allah ku gyara maganar nan da aka ce na bar Kano ne saboda rashin lafiya. Babu gaskiya a cikin wannan magana kwata-kwata. Ina cikin koshin lafiya. Ba na son rikici shi ya sa na bar jihar. Idan har na ci gaba da zama a Kano, ko fitowa na yi waje na san hakan zai haifar da matsaloli da yawa, wanda zai iya zama nakasu ga harkar tsaro a jihar. Ba na kaunar duk wani abu da zai haifar da tashin hankali har ta kai ga yin zanga-zanga. Lamarin da ya shafi zaman lafiya da tsaron rayukan jama’ata sun fi komai muhimmanci. Na bar Jihar Kano ne da niyya, babu wanda ya sa na bar Kano, babu kuma wanda zai hana ni komawa jihar. Zan iya komawa a duk lokacin da na ga dama. Babu wani ciwo da ke damuna.” Inji shi.
Rahotanni sun bayyana cewa a lokacin da ’ya’yan marigayi Sarki Ado Bayero suka je fada, a ranar Lahadi, don yin mubaya’a ga sabon sarki, Malam Muhamamd Sanusi II, Sanusi Ado Bayero ba ya cikinsu.
Da aka tambaye shi ko yaushe zai je fada don yin mubaya’a ga sabon sarki, sai ya ce, “Kamar yadda na gaya muku, babu wata matsala, ba ni so ne na zama sanadin tashin hatsaniya. Mutanen da ke bayanin cewa ban yi mubaya’a ba, saboda ba ni da lafiya, ba su da dalilin fadin haka. Lafiyata lau. Ni mai son zaman lafiya ne kawai. Mahaifinmu ya koyar da mu muhimmancin zaman lafiya.” Inji Ciroman na Kano.
Da yake bayani game da darasin rayuwa da ya koya a wajen mahaifinsa, Hakimin na Gwale ya bayyana cewa, “Mahaifinmu ya koyar da mu yadda za mu yafe wa jama’a idan suka saba mana. Ba abu ne na kare-jini, biri-jini ba.  Ba na kaunar duk abin da zai haifar da fitina ga jama’ata, komai girmansa ko kankantarsa. Zaman lafiya shi ne abin da muke ta kokarin zartarwa tsawon shekarun da muka yi.” Inji shi.
Idan za a iya tunawa, jim kadan da bayyana sunan Malam Sanusi Lmaido Sanusi  a matsayin sabon sarkin Kano rikici ya barke, musamman a kofar Kudu inda fadar sarki take. kura ta ci gaba da tashi bayan zaben tsohon gwamnan babban bankin, yayin da gwamnatin tarayya ta janye jami’an tsaro daga gidan gwamnatin Jihar Kano kuma aka sanya jami’an tsaro suka mamaye fadar sarkin suka hana motoci shiga da fita har zuwa ranar Alhamis da yamma inda suka janye.
A halin yanzu dai al’amuran sarauta sun fara komawa daidai a fadar Kano bayan rasuwar Sarkin Kano, marigayi Alhaji Ado Bayero da abubuwan da suka biyo bayan nada sabon Sarki Malam Muhammadu Sanusi na II.
Aminiya ta lura cewa al’amura sun fara daidaita a fadar ne tun daga lokacin da aka janye dimbin jami’an tsaron da aka jibge a kofar fadar, inda rundunar ’yan sanda ta ce ta yi haka ne don ta kare fadar daga masu iya kai hari ga fadar, sakamakon nada sabon Sarkin.
A ranar Asabar da ta gabata sabon Sarkin ya yi hawa irin na sarauta inda ya kai ziyara ga Mai Babban daki (wato mahaifiyarsa) da ke Unguwar Yakasai a birnin Kano.
A ziyarar da Aminiya ta kai fadar ta Kano, a ranar Talata, ta iske Mai martaba Sarkin Kano, Malam Muhammad Sanusi na II ya zauna a fada inda ya gana da hakimansa.
Kuma daga nesa da fadar ana jin kade-kaden al’adar gidan sarauta da ke nuna cewa Sarki na zaune a fada.
Aminiya ta ga yadda jama’a daga bangarori daban-daban na Jihar Kano da kuma kasa baki daya ke ci gaba da tururuwa zuwa fadar Sarkin don yi masa mubaya’a.
Daga cikin wadanda suka kai ziyarar goyon baya har da ’ya’yan marigayi Sarki Ado Bayero, lamarin da ya kawo karshen kace-nace da ake yi cewa ’ya’yan Sarkin ba su goyon bayan nadin Sarkin Muhammadu Sanusi na II.
Daga cikin ’ya’yan marigayi Sarkin da suka yi wa Sarkin Muhammadu Sanusi na II mubaya’a akwai Sarkin Dawakin Tsakar Gida, Hakimin Dala, Alhaji Aminu Ado Bayero da Hakimin Nasarawa, Alhaji Nasiru Ado Bayero da Hakimin Fagge, Alhaji Mahmud Ado Bayero da Hakimin Sumaila, Alhaji Ibrahim Ado Bayero da Hakimin kunchi, Alhaji Aliyu Ado Bayero.
Babban dan marigayin da ya nemi sarautar, Chiroman Kano, Alhaji Sanusi Ado Bayero bai je fadar ba, yana Abuja. Sai dai a tattaunawarsa da Aminiya ta tarho ya aike da sakon fatar zaman lafiya mai dorewa a jihar. “Muna yi wa jama’a godiya bisa yadda suka nuna alhininsu na rashin Mai martaba Sarki da kuma addu’ar nema masa rahama da suka yi. Haka muna yi musu godiya bisa kaunar da suka nuna mana. A karshe muna addu’ar Allah Ya zaunar da jiharmu da kasarmu lafiya,” inji shi.
Galadiman Kano, Alhaji Tijjani Hashim ya kai irin wannan ziyara ga Sarki Muhammadu Sanusi a fadarsa.
Mai alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Sa’ad Abubakar kuma ya tura tawaga ne don yi wa sabon Sarkin fatar alheri. Jagoran tawagar Magajin Garin Sakkwato, Alhaji Hassan danbaba ya ce sun je fadar ce don taya Sarki Muhammadu Sanusi murna bisa nadin da aka yi masa a matsayin Sarkin Kano na 14.