Gudun yamutsi ne ya hana ni zuwa rantsar da Abba —Ganduje
Gudun tada yamutsi daga magoya bayan Kwankwasiyya ne ya hana ni zuwa rantsar da Abba Kabir Yusuf.
Tsohon Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana cewar gudun yamutsin magoya bayan Kwankwasiyya ne ya hana shi halartar rantsar da sabon gwamna Abba Kabir Yusuf.
Ganduje ya bayyana haka ne a wajen bikin rantsar da shugaban kasa Bola Tinubu a dandalin Eagle Square da ke Abuja.
Ya ce: “Abubuwan kashi biyu ne: Akwai daya na mika takardu da za su nuna yadda aka gudanar da gwamnati da kuma irin abubuwan da aka kammala, da kuma wadanda suka rage ba a kammala ba da kuma shawarwari na gudanar da gwamnati daga ita sabuwar gwamnati mai shiga.
“Hawa na biyu, shi ne rantsarwa kamar yadda kike gani, to, saboda haka idan gwamnati mai tafiya ba gwamnatinsu daya da mai shigowa ba, to ba lallai ne a je a halarci rantsuwar ba.
“Domin idan an yi hakan akan samu yamutsi saboda magoya baya, dimokuradiyya ba ta kai yadda za a iya tafiyar da abun yadda ake gani a kasashen waje ba,” in ji Ganduje.
Game da alakarsa da sabuwar gwamnatin Kano da ta karbi mulki a ranar Litinin, Ganduje ya bayyana cewar rashin fahimtar al’umma ne kawai.
“Ai irin wannan rashin fahimar al’umma ne, amma kin san siyasa ba a raba ta da kace-na-ce. To, yawanci abin da ke faruwa ke nan. Akwai kyakkyawar alaka.”
Kazalika, ya musanta rade-radin da ake na cewar neman mukami ne ya sa yake yin tafiyar shugaban kasa Tinubu.
A cewarsa, “A’a ni ba na neman mukami nake ba, sai dai idan an ba ni mukami zan karba.”
Ganduje ya ce yana yi wa gwamnatin Tinubu fatan alheri da addu’ar samun nasara saboda zabar sa aka yi duba da ayyukan da ya yi lokacin da ya yi Gwamnan Jihar Legas.
Sai dai sabon Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya sha alwashin karbo duk wasu filaye da gidaje mallakin gwamnatin Jihar da aka mallaka wa wasu tsirarun mutane ba bisa ka’ida ba.
Ya bayyana hakan ne yayin da yake jawabi jim kadan bayan an rantsar da shi a matsayin sabon Gwamnan Jihar.