Gudunmawar Sarkin Kano Ado Bayero ga Bunkasa Musulunci

Musulunci ya shiga masarautar Kano ne a daidai lokacin da ya shigo kasar Hausa ko Afirka ta Yamma ta hannun fatake daga kasashen Larabawa ko Afirka ta Arewa. To amma bayyanar Musulunci a birnin Kano gadan-gadan ya fi shahara ne a yayin da wata tawaga ta malaman Musulunci a al’ummar Torankawa da Wangarawa ta sauka […]

Gudunmawar Sarkin Kano Ado Bayero ga Bunkasa Musulunci
Gudunmawar Sarkin Kano Ado Bayero ga Bunkasa Musulunci

Musulunci ya shiga masarautar Kano ne a daidai lokacin da ya shigo kasar Hausa ko Afirka ta Yamma ta hannun fatake daga kasashen Larabawa ko Afirka ta Arewa. To amma bayyanar Musulunci a birnin Kano gadan-gadan ya fi shahara ne a yayin da wata tawaga ta malaman Musulunci a al’ummar Torankawa da Wangarawa ta sauka a birnin Kano a tsakanin 1349 zuwa 1463 Miladiyya. Lokacin da fitaccen malamin nan Abdulkarim Almaghili ya isa Kano a zaman Sarki Muhammadu Rumfa ne Sarkin ya nemi ya wallafa masa wani littafi kan harkokiin mulki a Musulunci, inda ya rubuta masa mashahurin littafin nan mai suna ‘Taj Aldin Fi Ma Yajibu Alal Muluk’ da Mujaddadi Shehu Usman dan Fodiyo da kanensa Abdullahi suka ambata a rubuce-rubucensu.
Juyin juya hali da jihadin danfodiyo ya kawo ya ci gaba da kawo bunkasar Musulunci a masarautar Kano, kuma bayan jihadin ya ci gaba da bunkasa wani lokaci yana tuntube har Turawan Ingilishi suka shigo. A zamanin Turawan ne kuma Allah Ya albarkaci masarautar da wani muzakkarin sarki wato Sarki Abdullahi Bayero Sarki na 10 a Daular Fulani wanda ya aza tubalin kawo bunkasar Musulunci a masarautar, inda aka samu bunkasar ilimin addinin Musulunci aka fadada masallacin Juma’a na birnin Kano, kuma ya kafa mashahuriyar makarantar na ta Musulunci SAS. Kuma a zamaninsa ne aka samu matasan shehunnai kamar Sheikh Tijjani ’Yan Awaki da Sheikh Adamu Nama’aji da Sheikh Nasiru Kabara da Shehu Maihula (Allah Ya jikansu).
Wannan adalin Sarki shi ne mahaifin marigayi Sarki Ado Bayero, wanda shi ma ya bayar da gagarumar gudunmawa wajen bukasa addinin Musulunci a zamaninsa. Zamanin Sarki Ado Bayero ya kasance zamani na bunkasar Musulunci, tun daga makarantu da madaba’u da jaridu da mujallu da kungiyoyi da cibiyoyin Musulunci masu yawa.
A kashin kansa marigayi Sarki Ado Bayero ya bayar da gagarumar gudunmawa wajen yada addinin Musulunci ta hanyoyi daban-daban. Sananne cewa yakan yi tattaki zuwa duk wani taro da ke da alaka da addini a ciki da wajen Kano. Misali ya taba zuwa Uyo a Jihar Akwa Ibom don bude masallacin da Musulmin jihar suka gina, lamarin da ya jawo wa Gwamnan Jihar na lokacin Kanar Yakubu Bako bakin jini aka rika korafin ya je don mayar da jihar “Jihar Musulunci.” Mujallar Tambari ta 1 ga Shawwal 1415. BH.
Marigayi Sarki Ado kulluma yana sahun gaba wajen amsa kiran kungiyoyin Musulunci da ke kiran maguzawa zuwa ga addini, wannan ya sa jaridu da sauran kafafen watsa labarai ke ruwaito tattakin da yake yi don amsar sababbin musulunta. Misali a ranar 9/6/2000, saura kwana shida ya cika shekara 70 a duniya jaridar Gaskiya Ta Fi Kwabo ta buga labarin zuwansa kauyen Fammar da ke karamar Hukumar Kibiya don martaba maguzawa 300 da suka karbi Musulunci. Kuma kullum tambihinsa ga hakimai da dagatansa shi ne su mayar da hankali wajen kira maguzawa zuwa ga Musulunci.
A 1999 ne ya je karamar Hukumar Rogo ya za harsashin gina wata katafariyar cibiyar ilimin addinin Musulunci da kira zuwa ga Musulunci, inda ya ba ta gudunmawar Naira miliyan daya tare da alkawarin ci gaba da tallafawa har sai an kammala gininta. Kuma yadda yake halartar walimar da ake shirya wa sababbin musulunta yana matukar karfafa musu gwiwa, musamman yadda yake yin musabaha da su da karfafa musu gwiwa su tsaya kyam kan addini. Akwai wani lokaci ma da marigayin ya kaurace wa halartar wani taron sarakuna da masu fada-aji a zamanin mulkin Janar Abacha don halarar wani sha’ani na Musulunci a garin Kura.
A cikin birni marigayi Sarki Ado Bayero, bai gajiyawa wajen amsa gayyatar kafa gidauniyar ginin makarantu ko aza harsashinsu ko bude su. Misali lokacin bude makarantar Shabbabul kur’anil Muratta da ke Unguwar udun Nufawa, marigayi Sarkin hawa na musamman ya yi tare da wasu ’yan majalisarsa kamar Turakin Kano (yanzu Galadima) Alhaji Tijjani Hashim da marigayi Wazirin Kano Alhaji Shehu Gidado da dan Iyan Kano (yanzu Wambai) Alhaji Abbas Sanusi da wasu hakimai suka je har makarantar bisa dawaki. Duba jaridar Alkalami ta ran 31/3/1989.
Marigayi Sarki Ado Bayero ya bayar da gagarumar gudunmawa wajen kafa Majalisar Malamai ta Jihar Kano, wadda ta zama zuciyar Majalisar Malamai ta kasa. Wani karin abin sha’awa shi ne yadda fadarsa ke zama wata cibiyar harkokin addinin Musulunci, musamman lokacin azumin watan Ramadan, inda ake gabatar da tafsirin Alkur’ani Mai girma a kowace yamma da gidan rediyon Jihar Kano ke yadawa kai-tsaye.
A lokacin da ake tado da batun fadada aiki da shari’ar Musulunci marigayi Sarkin Kano ya ba da gagarumar gudunmawa don ganin an cimma nasara. Sarkin ya sha fitowa yana nuna goyon bayansa ga haka tare da karfafa wa gwamnatin jihar gwiwa ta hanzarta fadada aiki da ita.
A ranar 15/6/2000 da jaridar Gaskiya Ta Fi Kwabo ta yi hira ta musamman da marigayi Sarki Ado Bayero don cikarsa shekara 70 a duniya ya ce: “Babu wani dalili da wanda ba Musulmi ba, zai ce ba ya son a yi shari’ar Musulunci, saboda shari’a ba ta shafe shi ba. Kuma babu dalilin da wani Musulmi zai ce kada a yi shari’ar Musulunci, saboda shari’a ita ce ginshikin Musulunci.”
Sheikh Nasir Muhammad Nasir, Limamin Masallacin Juma’a na Fagge (Waje) ya ce gudunmawar Sarki Ado Bayero ga bunkasa Musulunci ba za su lissafu ba, ya kawo misali da cewa masallacin Juma’a daya ne kawai a birnin Kano, to amma da taimakon Sarkin yanzu haka (a shekarar 2000) a cikin birnin da kewayen Kano kawai. Ya ce, ba wanda zai iya cewa ga yawan masallatan Juma’a da ke cikin masarautar Kano wadanda mafi yawa Sarkin ne da kansa ya bude su.
Shi kuwa danmasanin Kano Dokta Yusuf Maitama Sule ya bayyana kokarin yada addinin Musulunci da bunkasa shi da marigayi Sarki Ado Bayero ya yi da cewa a cikin jininsa yake, tunda dai haka mahaifinsa Sarki Abdullahi Bayero ya yi.
danmasanin ya ce, saboda gudunmawar Sarki Abdullahi Bayero ga Musulunci har wani mawaki ke cewa: “Zamanin Sarkinmu an grika masallatai duk inda ka je sai Lazimi da Wazifa za ka ji.”
 Ya ce a zamanin Sarki Ado kuwa baa bin da ake yi sai bude masallatai da makarantun Islamiyya a kowane lungu na kasar Kano. Ya ce yanzu kusan kowane mako sai Sarkin Kano ya tafi bude masallaci ko makaranta a cikin gari ko kauye.     
Ya ce wani abin da ke karfafa gwiwa shi ne don mutunta al’amarin na addini Sarki har hawa yake yi in a cikin gari ne. danmasani ya ce ba halarta kawai Sarki Ado ke yi ba, har ma yakan bayar da gudunmawar dukiyarsa don daga kalmar Allah.
A irin wannan halartar harkokin addini ne ’yan bindigar da ake alakanta su da Boko Haram suka yi yunkurin halaka marigayi Sarkin a bara. Allahu Akbar yau mako guda ke nan da Allah Ya karbi ran wannan bawan Allah Sarki Ado Bayero yyana da shekara 84 a duniya. Allah Ya gafarta masa Ya yafe masa kura-kuransa, Ya sa Aljanna ta zama makomarsa.