Gudunmowar Kamaru a taron kungiyar Kare Harsunan Yammacin Afrika

kasar Kamaru na makwabtaka da gabar Yammacin Afrika, duk da cewa kuma kasar na tarayya ne da wasu kasashen tsakiyar Afrika da suka hada kungiyoyi daban-daban da suna neman ci gaban yankinsu. Ana kiyasta yawan daukacin al’umar kasar a kan miliyan 20. Sa’annan kuma tana kunshe da harsuna da yawansu ya dara 200, cikinsu har […]

Gudunmowar Kamaru a taron kungiyar Kare Harsunan Yammacin Afrika

Mahalarta a zauren taron Kungiyar Manazarta Harsunan Afrika Ta Yamma da aka gudanar a Ibadan, makon jiyakasar Kamaru na makwabtaka da gabar Yammacin Afrika, duk da cewa kuma kasar na tarayya ne da wasu kasashen tsakiyar Afrika da suka hada kungiyoyi daban-daban da suna neman ci gaban yankinsu. Ana kiyasta yawan daukacin al’umar kasar a kan miliyan 20. Sa’annan kuma tana kunshe da harsuna da yawansu ya dara 200, cikinsu har da Hausa; wanda yare ne na Yammacin Afrika da ’yan ci-rani suka yada shi a kasashe da dama na Afrika.
Duk da cewa babu alkaluma na hukuma da suka bayyana adadin Hausawa da suke kunshe a Kamaru, amma kuma ana kyautata zaton cewa yawansu ya kama kashi 2% na daukacin al’umma. Saboda haka, cudanyar da yaren ya yi da wasu yarukan Kamaru ya sa Hausar ta Kamaru ta ari wasu kalmomi daga yarukan, ta sanya a cikin Hausa.
Har ila yau kuma, baya ga yarukan cikin gida, Hausar ta Kamaru ta kunshi wasu kalmomi daga Faransanci da kuma Ingilishi, ganin cewa kasashen Faransa da kuma Ingila sun yi wa Kamaru mulkin mallaka. Kodayake kuma a hausance, ana samun yadda ake ambatar wadannan ababan; kamar na’ura mai kwakwalwa da za a ji cewa Hausawa na kira ‘Computer’ ko kuma ‘Ordinateur’ a faransace. Ko kuma jirgin ruwa ana kira ‘Ship’ ko kuma ‘Bateau.’ Hakannan ma kalmar jirgin sama mai saukar ungulu ba ta shiga cikin jerin kalmomin da akasari Hausawan Kamaru suke amfani da ita ba. A takaice dai har idan ya kama su yi amfani da Kalmar, suna aro ne kawai daga Turanci. ‘Helicopter’ ga Hausawan bangaren Arewa Maso Yamma da kuma Kudu Maso Yamma. ‘Helicoptere’ kuma ga sauran Hausawan sassan kasa.
Za a kuma iya rubanya misalai game da haka sosai. Daga cikin kalmomin da suke ba na Hausa ba kwata-kwata kuma da Hausawa a Kamaru suka shigar cikin yarensu akwai ‘Langa’ wato ‘Bokati’ ke nan, duk da cewa ita ma daga Turancin Ingila ta samo asali. Amma kuma ta Hausawar Kamaru ta zo ne daga ‘Longa’ da wasu kabilu da ake kira Yawundawa suke amfani da ita. Hausawan kuma suka musanya wasalin ‘o’ ya zama ‘a.’ Baya ga wannan kuma akwai kalmar ‘Mongo” a maimakon su ce yaron gida, wato mai yin hidima ke nan a biya shi a karshen wata. Wannan kalma ta ‘Mongo’ ta samo asali ne a yaren Yawundawa, har ila yau. Ma’anar wannan kuma ita ce yaro karami. Hausawa a Kamaru kuma na ambatar mace mai yin hidima a gida da suna ‘Monguwa.’
Irin wadannan misalan ne da kuma tarin wasu jama’a da suka zo daga sassan duniya daban-daban wurin halartar wannan taron suka karu da su.
Sai dai kuma Hausar Hausawan farkon da suka shigo Kamaru a karni ta 19, gabannin mulkin mallakar Turwan farko, wato Jamusawa. Wadannan Hausawan da suka yi ci-rani, sun yi kokarin kare harshensu. Hakan kuma ya sa wannan ya kubuta daga aron kalmomi daga yare makwabta. Ana iya fahimtar haka game da irin rashin maida hankali wurin neman ilimin zamanin da ba su kai yaransu sun yi ba. Sa’annan kuma sun dinga karantar da yaran al’adu na gargajiya, suna jan su a jiki tare da nuna musu muhimmancin haka. Abin da ya sa ke nan har zuwa wani lokaci kamar, sashen shekara ta 1975, Hausar Hausawan Kamaru ba ta samu badda kamanninta ba daga Hausa ta asaliya.
Yadda mutanen farko suka dinga yi, a makarantun allo da Hausa ake fara ilimantar da yara da yaren Hausa. Ana karantar da su harrufa da Hausa, gabannin su fara nakaltarsu da Larabci. Abin da ake kira da suna babbaku ke nan. Sa’annan kuma an dinga karantar da su yadda za su dinga bambanta jinsi idan suna magana, kada su dinga dagula su. Su kira namiji da suna mace, ko kuma sabanin haka. A yanzu haka abin da yake gudana ke nan.

Bin diddigi: Gaskiyar batun kai hari a Bankin CBN

NAJERIYA A YAU: Lakurawa muka kai wa hari a Sakkwato —Sojoji

Manyan alhinin Najeriya a 2024

’Yan sanda sun kama waɗanda suka shirya rikicin ‘yan daba a Kano