Gudunmuwar matan Hausawa ga rushewar aure

Ko shakka babu a yau  mata suna bada muhimmiyar gudunmuwa wajen rushewar aure.   Zaman aure zama ne na  juriya da hakuri, zo mu zauna zo mu saba. Yau da gobe sai Allah. Duk da cewa yanzu mata suna kokari wajen neman Ilimin addini da na zamani, sai dai ba su cika amfani da Ilimin nasu […]

Gudunmuwar matan Hausawa ga rushewar aure
Gudunmuwar matan Hausawa ga rushewar aure

Ko shakka babu a yau  mata suna bada muhimmiyar gudunmuwa wajen rushewar aure.   Zaman aure zama ne na  juriya da hakuri, zo mu zauna zo mu saba. Yau da gobe sai Allah. Duk da cewa yanzu mata suna kokari wajen neman Ilimin addini da na zamani, sai dai ba su cika amfani da Ilimin nasu ba wajen ganin auren su ya yi karko ba, da an yi aure shekara daya, biyu uku, sai ka ga aure ya lallace, wani ma ko shekarar ba a yi, yanzu za ka ga wasu matan ba su cika sa tsoron Allah a cikin zukatansu da  zamantakewarsu da mazajensu ba, su dauka aure ibada ne, gidan miji gidan neman lahira ne ba wajen cin kasuwa ne ba.   Duk abin da kika ga ba ya so to ki guje shi ki nuna masa kin fi shi rashin son wannan abin.  In ko ya nuna yana son abin to ki nuna masa kin fi shi son abin, in za ki fita to nemi izninsa in ya bar ki ki je, in bai bari ba ki hakura wani lokacin kin je.
A wannan zamani za ka ga mace za ta yi wa miji laifi, amma lokacin da za ka nuna mata sai ta fi ka fada, ko ka ga suna fice- fice marasa amfani ba tare da sun nemi izini ba, amma ba ka da ikon yin magana sai ka ji sun ce kana neman raba zumunci, wani lokacin ma su ke matsa wa mazajensu lalle sai sun sake su ba tare da wata kwakkwarar hujja ba, su a ganinsu, su fito suna yawon zawarci, lungu da sako ana kallon su ya fi musu, Wa’iyazubillah.
Haba mata iyayen al ‘umma, yaushe ne za ku hankalta, yakamata ku gyara don kuna da sauran lokaci. Shekara goma zuwa sha biyar da suka gabata abin ba haka yake ba.
A zamanin da za ka ga an yi aure, ko da matar ba ta taba ganin mijin ba, kuma haka za ta yi hakuri ta zauna da shi ko ba ta so, kuma auren ya yi al’ barka, duk da yake Ilimi yayi karanci tare da wasu a wancan lokaci, amma ana kwatanta amfani da shi, sannan akwai ladabi da biyayya da dabi ‘a mai kyau, mata suna daraja aure, amma yanzu abin ya canza.To ya za a yi a gyara?
Babban abinda zai kawo mana mafita, shi ne mata su dauka cewa aure ibada ne kuma ana samun aljanna idan an bi Allah an kyautata wa miji, ban da dora wa miji abinda ya fi karfinsa.   A guji sanya karya da rashin gaskiya, a rika kudurtawa cewa za a yi aure ne na har abada,duk da cewa su ma mazan da nasu laifin, amma mata su ne gaba wajen ba da matsala.   Idan muka ga yadda Allan Ya ba mata baiwa wajen zama da miji ko ya yake za ta iya canza shi ta samar masa natsuwa  ka same shi kullum hakalinsa a natse, kamar yadda Hausawa ke cewa ‘matar na tuba ba ta rasa mijin aure’.
Sannan iyaye ma da nasu aikin wajen bai wa ‘ya’yansu Ilimi da tarbiyya ta-gari,da nuna masu yanayin zaman duniya, sannan idan sun aurar da su kafin su tare su yi musu huduba ta hanyar nuna masu mahimmancin aure da tsoran Allah a rayuwa, domin idan auren bai yi karko ba to gidan iyayan za su dawo, wajen hudubar da ka yi mata kamar yadda shara ‘a ta koyar.
Haka kuma malamai su cigaba da kokari wajen fadakar da mata muhimmancin yin ladabi da biyayyar aure da da’ a ga miji,idan suka ki yin haka su nuna musu irin halin da za su tsinci kansu a ranar gobe kiyama, Allan ya kyauta.
Allah Ya ba mu ikon kiyayewa, Ya shiryar da mu da zuri ‘armu, Ya ba mu zaman lafiya, hakuri da kwanciyar hankali, amin.
Muhammad Kabir Salisu, Gazarawa Communication Center Katsina, 08034200141