Gudunmuwar Sarakunan Gargajiya Wajen Hada Kan Al’umma (2)

Babu shakka zamani ya zo wa nahiyarmu da sauyi, inda wasu daga cikin al’ummarmu na zamanin nan ba su san kima da darajar sarakunan gargajiya ba, domin kuwa ba su san irin tsarin da ya gudana ba ta fuskarsu, kafin zuwan mulkin Turawa. A kashi na biyu na wannan jirwaye mai kamar wanka, marubucinmu kuma […]

Gudunmuwar Sarakunan Gargajiya Wajen Hada Kan Al’umma (2)
Gudunmuwar Sarakunan Gargajiya Wajen Hada Kan Al’umma (2)

Babu shakka zamani ya zo wa nahiyarmu da sauyi, inda wasu daga cikin al’ummarmu na zamanin nan ba su san kima da darajar sarakunan gargajiya ba, domin kuwa ba su san irin tsarin da ya gudana ba ta fuskarsu, kafin zuwan mulkin Turawa. A kashi na biyu na wannan jirwaye mai kamar wanka, marubucinmu kuma saraki, MALAM ISHAkA SARKIN FULANI DANKAMA (08100006858), ya rubuto cewa:

Bayan wannan kuma kowane shugaba yana kasancewa ne bisa cancantarsa. Ma’ana, sai wanda ya cancanta zai nemi shugabanci; kamar yadda su ma jama’a suke zaben wanda suka yi imani shi ne ya fi dacewa. To, mutum ya nemi a dora shi a kan mukami domin ya cancanta, su kuma jama’a su dora masa nauyin hangen zai iya; shi yakan sanya shugabanni yin bakin kokarinsu don ganin sun kyautata wa al’ummarsu.
Har wa yau wannan zai kasance kamar tarnaki a gare su, ta yadda ba za su yi komai suka ga dama ba, wato babu wuce gona da iri. A kan haka lallai ne komai za su gudanar ya kasance bisa tafarkin da jama’arsu suka amince a kai.
Canje-Canjen Da Suka Auku Ga Ayyukan Sarakuna:
A farkon karni na ashirin, 15 ga watan Maris 1903, Turawan mulkin mallaka suka karbe mulkin Daular Usmaniyya. Tun daga wannan lokaci aka fara samun canje-canje dangane da ayyukan sarakuna. Turawa sun san ba za su iya mulkar jama’a kai tsaye ba, don haka suka bullo da wani sabon salon mulki. Wato sai suka bar sarakuna suka “ci gaba” da mulki amma kuma su suke ba sarakuna umarni.
Daga baya kuma sai gwamnati ta aika da wakilanta, wato D.O-D.O da Rasdan-Rasdan, wadanda za su yi aiki tare da sarakunan. Sai dai a bangaren shari’a kodayake an kafa kotunan majistare, kararrakin da suka danganci rabon gado da aure da sauransu sun kebanta ga kotunan alkalai ne.
A shekarar 1954 ne aka kafa N.A-N.A. A wannan lokaci ne aka kafa sarki da ’yan majalisa, wato maimakon sarki da majalisarsa da ake da ita a da. Manufa, ba kamar a da ba lokacin da sarki “shi ne wuka, shi ne nama” a yanzu kusan dukkan abin da sarki zai aiwatar sai ya sami amincewar ’yan majalisa. Wannan tsari ne ya ci gaba har bayan karbar mulkin kai a shekarar 1960.
A shekarar 1968 ne aka kafa dokar majalisan yankunan mulki a kasa baki daya. A wannan lokaci ne aka karkasa kasashen sarakuna zuwa yankunan mulki, sannan aka nada kantomomi. Su wadannan kantomomin ne suke gudanar da mulki amma suna neman shawarar sarakuna. Har wa yau a wannan lokaci ne aka karbe kotu da kurkuku da ’yan sanda da kuma baitul mali daga hannun sarakuna.
Sannan a shekarar 1976 aka kirkiro kananan hukumomi. A wannan tsari, jama’a za su yi takara a zabe su domin su wakilci mutanensu a majalisa. Wadannan wakilai su ne suke gudanar da dukkan abubuwan da suka shafi jama’a. Wannan tsari shi ne ya ci gaba har zuwa shekarar 1979, lokacin da aka kafa Majalisar Sarakuna a kowace jiha kuma aka sanya a kundin tsarin mulki. Kusan wannan shi ne halin da ake ciki har kawo yau.
Taimaka Wa Hada Kai Babu shakka, sarki shi ne mutum na farko wanda yake kokarin ya ga mutanensa sun hada kansu waje daya sun zama tsintsiya madaurinki daya. Ya fi kowa jin dadi ya ji an ce jama’arsa suna zaune lafiya, babu fada babu tsegunguma. Arziki da wadata ba su wanzuwa ga kasa, sai idan akwai hadin kai da zaman lafiya.
Kafin zuwan Turawan mulkin mallaka, majalisar sarki ba dakin shawara ce kawai ba, nan ne kuma kotun koli inda ake sauraron shari’o’in da aka daukaka daga kotunan alkalai a ko’ina cikin kasarsa. A irin wannan zama ne ’yan majalisar sarki, a karkashin shugabancinsa suke tattaunawa a kan matsalolin da aka samu daga wani yanki na kasar; sannan su ba da shawara kan abin da suka ga ya dace. Haka kuma wani lokaci ’yan majalisar, irin su Wali da Liman, sukan ba da fatawa a kan wasu hukunce-hukunce na shari’a.
Alal-hakika duk da canje-canjen da aka samu kawo yanzu, sarakuna suna da gagarumar gudunmuwa da suke bayarwa wajen hada kan al’umma. A ko yaushe hukuma ta yi nufin gudanar da wani al’amari da ya shafi jama’a, tana bi ne ta kan sarakuna; ganin su ne suka fi kusa da jama’a. Misali, shirye-shiryen gwamnati irin su kidaya da canjin kudi da allurar riga-kafi da sauran abubuwa dangin wadannan. Kai, hatta sasanta tsakanin al’ummomi da aka samu rashin jituwa; ko kuma wayar da kan jama’a  a kan wasu manufofi na gwamnati da ake ganin sun saba wa al’ada. A duk lokacin da aka samu irin wadannan abubuwa, sarakuna ake sanyawa a gaba su wayar wa jama’a da kai ko su rarrashe su.
Har wa yau kuma sarakuna su ne rumbun al’adunmu na gargajiya. Yanzu haka mutum ya je fada zai ga wasu nau’o’in al’ada a bayyane da suka hada da tsarin gine-gine da tufafi da nau’o’in abinci da abubuwan hawa, musamman dawaki da kayansu da sauransu. Wadannan kuwa duk wasu alamu ne na hada al’adunmu kyawawa masu kara tabbatar da asalinmu da ke hada yaukaka zumuncinmu da jin dadinmu.
Haka kuma har yanzu mutane da dama suna dogaro da sarakuna ne da wasu harkoki na addini. Sarakuna garkuwoyin addinin Musulunci ne domin sukan zama kansakaloli masu hada al’umma a tafarkin addinin Musulunci. Mun ga misalai da yawa na shugabanninmu, magabata a wannan kasa, wadanda suka tsayu ainun a kan jaddada wa mutane riko da Musulunci, wanda yake igiya daya wadda a kanta kowa zai yi riko.
Bisa takaitawa, sarakuna suna bayar da gagarumin taimako domin ganin sun hada kan al’ummominsu ta hanyoyi kamar wadannan:
1-Kira a matsayin abu daya ga addinin Musulunci. 2-karfafa zumunci da kyautata zumunta wadda wata babbar sila ce ta karfafa al’umma ta zama abu daya. 3-Yaukaka son juna da taimakon juna domin wasu matakai ne da suke tsarkake al’umma daga fadace-fadace ko zargin juna da sukan haddasa darewar jama’a. 4-Kwantar da tarzoma da kira ga samar da zaman lafiya. Wato a kullum sarakuna mutane ne masu kokarin yayyafa wa kura ruwa don ta kwanta. 5-Su turaku ne na samar da zaman lafiya a kowane lokaci, tun ma ba a lokacin wani tashin hankali ba.