Guguwa ta hallaka mutum 11 a Pakistan
Jami’an aikin ceto sun fuskanci kalubale saboda nisa da kuma wahalar zuwa yankin.
Akalla mutane 11 daga wata kabilar makiyaya ciki har da wani yaro dan shekara hudu suka mutu sakamakon mahaukaciyar guguwa a Arewacin Pakistan.
Dusar kankara ta fado a lokacin da ’yan kungiyar suka tsallaka wani yanki mai tsaunuka tare da garken awakinsu.
- Dan Najeriya ya saya wa karensa motar Naira miliyan biyu
- Rashin tsari da makabartun Kano ke fama da shi
An kuma samu jikkatar wasu mutane 25, inda ake ci gaba da aikin ceto.
Firaministan Pakistan, Shehbaz Sharif ya bayyana alhininsa game da mutuwar mutanen, inda ya ce al’amura irin su kankara na karuwa saboda sauyin yanayi.
Ruwan sama kamar da bakin kwarya ya afku ne da sanyin safiyar ranar Asabar a wani bangare na hanyar da ta bi ta gundumar Astore na yankin Gilgit Baltistan zuwa makwabciyarta Azad Kashmir, a yankin Kashmir da ke karkashin Pakistan.
Wasu mata hudu da yaro dan shekara hudu na daga cikin wadanda suka mutu, kamar yadda babban jami’in ’yan sanda Ziarat Ali, ya fada wa Kamfanin Dillancin Labarai na AFP.
Bayanai sun ce jami’an aikin ceto sun fuskanci kalubale saboda nisa da kuma wahalar zuwa da yankin yake da shi.