Guguwa ta lalata gidaje sama 9,000 a Adamawa

Hukumar ta gargaɗi mutanen yankunan da lamarin ya shafa kan komawa gidajensu ba tare da izinin gwamnati ba.

Guguwa ta lalata gidaje sama 9,000 a Adamawa

Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Ƙasa (NEMA), ta bayyana cewar aƙalla sama da gidaje 9,733 ne, guguwa ta lalata a Jihar Adamawa.

Shugaban ayyuka na NEMA a Adamawa, Mista Ladan Ayuba ne, ya bayyana hakan a wata hira da kamfanin dillancin labaran Najeriya (NAN), a Yola.

Ya ce hukumar ta tantance ƙananan hukumomin da abin ya shafa da suka haɗa da; Jada, Hong, Mayo-Belwa, Madagali da Fufore.

Ayuba ya kuma buƙaci mazauna yankunan da ambaliyar ruwan ta shafa da su koma wasu wurare domin kare lafiyarsu.

Ya ce gargaɗin ya zama wajibi ne, saboda hasashen da NiMet ta yi cewa Adamawa na cikin jihohin da za su fuskanci ambaliyar ruwa a 2024.

Ayuba ya ƙara da cewa, yankunan da ake iya fuskantar matsalar sun haɗa da ƙananan hukumomin Fufore, Yola-Arewa, Yola-kudu, Girei, Numan, Lamurde da Gombi.

“Don kare lafiyarku, da fatan za ku guje wa wuraren da ambaliyar ruwa ta fi ƙamari, ku tsaya a kan tudu mai tsayi kuma ku daina zubar da shara a magudanan ruwa,” in ji shi.

Jami’in na NEMA, ya kuma shawarci mazauna yankin da su rungumi ɗabi’ar sauraron rediyo domin samun bayanan da suka dace daga hukumar.

“Har ila yau, kada ku sha ko mwanke tufafi da ruwan ambaliya don gujewa kamuwa da cutar kwalara.

“Mutane za su koma gidajensu ne kawai lokacin da hukumomi suka ce ba su izninin komawa saboda muna fuskantar ambaliyar ruwa sakamakon sako ruwa daga dam ɗin Lagdo a Jamhuriyar Kamaru”, in ji shi.

Ayuba, ya buƙaci shugabannin gargajiya da su ƙara ƙaimi wajen isar da saƙon gwamnati ga al’ummarsu domin wasu ba sa sauraren kafafen yaɗa labarai.