Guguwa ta yi sanadin rasuwar mutum 2, ta lalata gidaje a Yobe

Mutanen yankin sun nemi ɗauki daga gwamnatin jihar.

Guguwa ta yi sanadin rasuwar mutum 2, ta lalata gidaje a Yobe

Aƙalla mutum biyu ne suka rasu, yayin da wasu suka jikkata sakamakon ruwan sama mai ƙarfi da iska suka auku a garin Gashuwa, da ke Ƙaramar Hukumar Bade a Jihar Yobe.

Lamarin, ya faru ne da yammacin ranar Laraba, inda guguwar ta lalata gidaje, shaguna, wuraren kasuwanci da wasu gine-ginen jama’a.

Wata majiya daga garin ta shaida wa Aminiya cewa lamarin ya janyo asarar dukiyar miliyoyin naira, tare da raba wasu mazauna yankin da matsugunansu.

Shugaban Ƙaramar Hukumar Bade, Ibrahim Babagana, ya bayyana lamarin a matsayin ƙaddara daga Allah, yana mai cewa guguwar ta haifar al’ummomin yankin koma baya.

Ya ce rufin gidaje da dama sun buɗe, wasu shaguna sun rushe, yayin da magidanta da ’yan kasuwa suka rasa muhimman kayayyaki da hanyoyin samun abin dogaro da kai.

Shugaban Ƙaramar Hukumar ya ce girman ɓarnar ya wuce ƙarfin Ƙaramar Hukumar, don haka ake buƙatar taimakon gwamnatin jihar wajen samar da kayan agaji da matsugunin wucin gadi ga waɗanda abin ya shafa.

Wani mazaunin Gashuwa, Mustapha mai sana’ar kayan miya, ya ce ba yawan ruwan sama ne ya fi jawo ɓarnar ba, face iska mai ƙarfi.

Ya ce gidaje da dama sun lalace, yayin da wasu kayayyakin sadarwa suka samu matsala sakamakon guguwar.

Mustapha ya danganta yawaitar irin wannan iska mai ƙarfi da raguwar bishiyoyi a yankin da ke kusa da hamadar Sahara.

Ya bayyana cewa bishiyoyi suna taimakawa wajen rage ƙarfin iska da kare muhalli, amma sare su saboda noma, faɗaɗa gari da neman itacen girki ya sa yankunan fuskantar matsalolin muhalli.

Wasu mazauna yankin sun bayyana guguwar a matsayin ɗaya daga cikin manyan iftila’i da suka taɓa faruwa a Gashuwa, inda suka ce mutane da dama sun rasa gidaje..

Sai dai Daraktan Lafiya na Babban Asibitin Gashuwa, Dokta Akinola Adekunle, ya tabbatar da cewa mutane biyu ne suka mutu, yayin da wasu da dama suka samu raunuka.

Ya ce dukkanin waɗanda suka jikkata sun samu kulawar likitoci kuma an sallame su daga asibitin.

A nata ɓangaren, Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Jihar Yobe (SEMA), ta bayyana cewa guguwar ta shafi wasu al’ummomi a Ƙananan Hukumomin Bade, Yunusari da Bursari.

Hukumar ta ce ta tura jami’an agaji da ’yan sa-kai domin tantance ɓarnar da aka yi da kuma gano irin taimakon da waɗanda abin ya shafa ke buƙata.