Guguwar Buhari ba ta ba PDP tsoro – Hussaini Jalo

Barista Hussaini Mamman Jallo shi ne Ko’odinetan Kwamitin Yakin Zaben Shugaba Jonathan da Namadi Sambo a Jihar Kaduna, a tattaunawarsa da manema labarai ya bayyana cewa Jam’iyyar PDP ce za ta sake kafa gwamnati a kasar nan inda ya musanta zargin da ake yi musu cewa suna amfani da karfi wajen cin zabe: Kwanan nan […]

Guguwar Buhari ba ta ba PDP tsoro – Hussaini Jalo
Guguwar Buhari ba ta ba PDP tsoro – Hussaini Jalo

Barista Hussaini Mamman Jallo shi ne Ko’odinetan Kwamitin Yakin Zaben Shugaba Jonathan da Namadi Sambo a Jihar Kaduna, a tattaunawarsa da manema labarai ya bayyana cewa Jam’iyyar PDP ce za ta sake kafa gwamnati a kasar nan inda ya musanta zargin da ake yi musu cewa suna amfani da karfi wajen cin zabe:

Kwanan nan Shugaba Jonathan ya tabbatar wa jama’ar kasa cewa zaben 2015 ya fi kowane zafi. Kana ganin za ku kai labari?

Ai ko kansila kake nema a yanzu kai ko Sarkin Kasuwa ne dole ka san akwai kalubale. Zabe ba abin wasa ba ne, zabe wani abu ne da dole ka roki Allah Ya ba ka nasara. Kuma yadda zaben bana ya zo akwai sauyi ba irin na da ba, amma ko shakka babu duk da kalubalen Allah zai yi mana maganinsa kuma PDP za ta ci zabe.
Batun cin hanci da rashawa a wannan gwamnati na daya daga cikin batutuwan da suka janyo wa jam’iyarku bakin jini inda har tsohon Shugaban kasa Obasanjo ya yi magana, amma kamar Shugaba Jonathan bai shirya yin komai a kai ba, me za ka ce?
Cin hanci da rashawa kwarai ya yi katutu a Najeriya kuma gwamnati ba za ta iya kawar da shi baki daya ba a kasar nan, domin abu ne da ya shafi kusan duk fannonin rayuwar jama’a ba ’yan siyasa kadai ba har da ga ma’aikatan gwamnati. Akwai wadanda gwamnati ta kore su, akwai kuma wadanda a yanzu suna hannun Hukumar EFFC. Sai dai na san gwamnatin na iya kokarinta na kawar da cin hanci a kasar nan.
Me za ka ce game da zargin lalata fastocin ’yan takara da kuma furta kalamai marasa dadi a lokacin yakin neman zabe?
Wannan zance na yage fastoci da kuma furta kalamai marasa dadi da wasu ke yi, shi ke kara tsorata mutane har wasu ke neman barin gari (ko kasa) har sai bayan zabe. Mu dai abin da muka ce shi ne Allah Ya bai wa kowa damar shiga jam’iyyar da yake so, saboda haka a bai wa kowa damar yin siyasar da yake so. Kowa ya manna fostarsa inda yake so, kowa ya manna kyallensa ko kafa tutarsa inda yake. Sannan ranar zabe kowa ya samu damar zuwa ya zabi ra’ayinsa. A daina tilasta wa mutane su yi jam’iyya domin wane kaza yana jam’iyyar, idan wane kazan da ke jam’iyyar mutumin kirki ne ba kowa ba ne da ke jam’iyyar mutumin kirki. Kuma a daina kafirta ’yan PDP domin abin an kai wani yanayi da idan mutum ya shiga PDP sai a kafirta shi ko a ce ka yi ridda. Wannan ba siyasa ba ce kuma ba daidai ba ne. Saboda haka zan yi kira ga abokan adawa cewa ba ma yaga fosta sai an yaga mana.
Bama yaga bana sai an yaga mana. An farfasa mana motoci amma duk da haka sai muka kirawo ’yan jam’iyyarmnu muka bukaci su zauna lafiya kada kuma su yaga wa kowa fostarsa ko banarsa kuma kada a fasa motar kowa, amma fa idan aka yi mana ba za mu bari ba, amma idan aka bar kowa ya yi ra’ayinsa sai a zauna lafiya. kasa ma za ta zauna lafiya za ka ga harkar siyasar ma ta canja domin ba a tilasta wa mutum ya zabi wanda ba ya so sai dai ya zabi ra’ayinsa.
Ana zargin cewa PDP za ta yi amfani da karfinta wajen cin zabe, me za ka ce?
Zancen yin amfani da karfi bai taso ba, domin PDP ba ta amfani da karfi wajen cin zabe sai dai ta yi amfani da kuri’un jama’a. Maganar amfani da karfi bai taso ba tunda Hukumar Zabe ce za ta shirya zabe kuma za a je a yi zaben. Kuma Allah zai ba PDP nasara in Allah Ya yarda, amma PDP ba ta amfani da karfi wajen cin zabe sai dai kuri’ar jama’a.
Yaya kuke shirin tunkarar guguwar Buhari a wannan zabe mai zuwa?
Kowa ba ya son guguwa ko kai ma nan ba ka son guguwa domin idan ka ga guguwa gudu za ka yi domin guguwa ba abin alheri ba ne. Mu iska muke son shaka mai sanyi wadda za ta kara mana lafiya. Guguwa mu ba ta ba mu tsoro domin ba yanzu aka fara yi mana barazana da guguwar Buhari ba. Wannan barazana ba za ta ba mu tsoro ba, iska muke so mu shaka mai sanyi da za ta ba mu lafiya. Shi ya sa muke kira ga ’yan kasa da zu bi iskar Jam’iyyar PDP domin su ci gaba da samun romon dimokuradiyya a kasar nan.
Akwai batun cewa jama’a na sayar da katin zabensu, yaya kake ganin za a magance wannan matsala?
Jama’a na da ’yancin yin zabe, amma idan mutum ya sayar da katinsa ka ga ke nan ya sayar da ’yancinsa na zabar shugaban da yake so. Idan ka sayar da katinka gobe idan shugaban da aka zaba bai yi maka ba, ba ka da bakin magana. Don haka zan yi amfani da wannan dama wajen kira ga ’yan kasa cewa kowa ya rike katin zabensa domin da shi za ka iya zabar wanda kake so. Baya ga zabe ma nan gaba a kasar nan ana iya cewa ba za a yi maka wani abu ba sai ka nuna katin zabenka. Ka ga ke nan idan ka sayar sai ka yi da na sani.
Batun tsaro na daya daga cikin manyan kalubalen da wannan gwamnati ke fuskanta, yaya kuke ganin wannan batu?
Harkar rashin tsaro wata annoba ce da ta damu duniya baki daya ba wai Najeriya kadai ba. Idan ka duba ai ba a san da wani abu wai ISIS ba, amma kwanan nan ta shigo, saboda haka batun rashin tsaro abu ne da Allah Ya kawo saboda haka duk wanda yake Najeriya dan PDP ne kai ko APC ko APGA kai da wanda ba shi da jam’iyya akwai bukatar mu ci gaba da addu’I’on Allah Ya kawo karshen wannan fitina. Kuma gwamnatin Shugaba Jonathan da Namadi Sambo tana kokarin ganin an magance matsalar. Kuma hadin gwiwar da Najeriya da Nijar da Chad da Kamaru wajen tunkarar matsalar ya taimaka matuka wajen samun nasarori don kawo karshen abin. In Allah Ya yarda da taimakon ’yan kasa da addu’o’in da jama’a ke yi da tashi tsaye da Gwamnatin Tarayya ta yi in Allah Ya yarda wannan rikici na Arewa maso Gabas zai zama tarihi.
Shugaban kasa da Gwamna suna fuskantar kalubale a Jihar Kaduna, ba ka ganin laifinku ne ’yan siyasa na kin yin abin da ya kamata ku yi tun a baya sai yanzu kuke fargar jaji?
Babu wata maganar kalubale dama idan zabe ya zo akwai barazana da abokan adawa ke yi domin ba mutane tsoro ko su ba jam’iyya mai ci ko gwamnati tsoro. Mu kuma duk wata barazana da tashin hankali ba za su tsora ta mu ba, domin mun saba ganin irin wadannan abubuwa. Kuma duk wani abu da PDP ya kamata ta yi an yi wa mutunen kasar nan. Hanyoyi da inganta harkokin lafiya da ilimi da wutar lantarki da samar da taki da sauransu. Babu yadda za a ce an kammala komai dari bisa dari domin kowa ya san tattalin arzikin duniya ya yi kasa haka ma tattalin arzikin Najeriya ya yi kasa. Wannan ya sa wasu daga cikin abubuwan da aka tsara za a yi ba su yiwuwa, ba wanda kuma aka fara ba a karasa ba, amma da zarar tattalin arziki ya inganta za a ci gaba da ayyukan raya kasa. Saboda haka babu wani kalubale da za su tsora ta mu game da zaben Shugaban kasa da Gwamna Ramalan Yero a jihar nan insha Allahu.