Guguwar Dorian ta hallaka mutum 5 a Bahamas
A kalla mutum biyar ne suka rasu, yayin da Guguwar Dorian ke ci gaba da lalata sassan Tsibirin Bahamas. Masu hasashen yanayi sun yi gargadin cewa Guguwar Dorian ka iya ci gaba da tafka barna a Tsibirin Bahamas. Firayi Ministan Kasar, Hubert Minnis ya ce an tabbatar da mace-macen ne a tsibirin Abaco, wanda ya fi […]
Guguwa da ambaliyar ruwa da ta afkawa Tsibirin Bahamas
A kalla mutum biyar ne suka rasu, yayin da Guguwar Dorian ke ci gaba da lalata sassan Tsibirin Bahamas.
Masu hasashen yanayi sun yi gargadin cewa Guguwar Dorian ka iya ci gaba da tafka barna a Tsibirin Bahamas.
Firayi Ministan Kasar, Hubert Minnis ya ce an tabbatar da mace-macen ne a tsibirin Abaco, wanda ya fi jigata daga barnar guguwar.
Kungiyar agaji ta Red Cross ta ce gidaje kimanin dubu 13, ake tsammanin sun lalace zuwa yanzu.
Shugaba Minnis ya ce har yanzu wannan guguwa ta Dorian na da matukar hadari.
Ana ganin yadda ruwan da ya yi ambaliya ke kara tudadowa, yana wancakali da motoci da itatuwa.
Rahotanni na nuni da yadda ambaliya ta mamaye kusan ko’ina, inda wadansu mutane ke hawa rufin gidajensu domin gudun kada ruwa ya shanye su a kasar.
Dorian ita ce guguwa mafi karfi da ta fada wa Tsibirin Bahamas, sannan masana yanayi na sa ran za ta matsa zuwa gabar Amurka ta Gabas.