Guguwar ficewa daga APC ta tafi da Tom Ikimi da Sanata Lanlehin
Guguwar ficewa daga babbar jam’iyyar adawa ta APC ta yi awon gaba da tsohon Ministan Harkokin Waje kuma jigo a jam’iyyar Cif Tom Ikimi da kuma Sanata mai wakiltar Oyo ta Kudu Sanata Olufemi Lanlehin.Cif Ikimi wanda ya bayyana ficewarsa daga APC a ranar Talata, bai fadi jam’iyyar da zai koma ba, yayin da Sanata […]
Guguwar ficewa daga babbar jam’iyyar adawa ta APC ta yi awon gaba da tsohon Ministan Harkokin Waje kuma jigo a jam’iyyar Cif Tom Ikimi da kuma Sanata mai wakiltar Oyo ta Kudu Sanata Olufemi Lanlehin.
Cif Ikimi wanda ya bayyana ficewarsa daga APC a ranar Talata, bai fadi jam’iyyar da zai koma ba, yayin da Sanata Lanlehin ya koma Jam’iyyar Accord Party (AP) a wani gangami da aka gudanar a Ibadan a ranar Talatar.
Cif Ikimi ya fadi a wata wasika da ya rubuta wa Shugaban Jam’iyyar APC ta kasa, Cif John Odigie-Oyegun, mai kwanan wata 26 ga Agusta, cewa ya gode kan wasikar da aka aika masa a ranar 15 ga Agusta don halartar taron jiga-jigan APC na kasa da kuma Kwamitin Amintattu na APC, inda ya yi nadamar rashin halartarsa, to amma yana sanar da shi ficewarsa daga Jam’iyyar APC daga ranar.
Cif Ikimi dan rusasshiyar Jam’iyyar ACN ce da ta hade da jam’iyyun CPC da ANPP da wani bangare na APGA, don tada Jam’iyyar APC.
Ya jagoranci tarurrukan hadin gwiwar jam’iyyun don tsara hadewar a gidansa na Abuja, kuma ya so tsayawa takarar zama shugaban jam’iyyar ta kasa a babban taronta na kasa a watan Yuni, amma aka yi zargin wasu shugabannin jam’iyyar ciki har da tsohon Gwamnan Jihar Legas Cif Bola Tinubu wanda ya goyi bayan Odigie-Oyegun suka dakile shi.
Cikin fusata ya kaurace wa taron kuma bayan kwanaki ya fitar da wani bayani yana zargin Tinubu da kanainaye jam’iyyar tare da bayyana zaben da ya kawo Odigie-Oyegun a matsayin wasan yara.
Ya ce gwamnonin jam’iyyar sun hada kai da Tinubu wajen rusa tsarin dimokuradiyya a babban taron, kuma ya zarge su da rarraba mukamai a tsakaninsu ta hanyar da ba ta kamata ba.
Ikimi ya zargi gwamnonin da kirkiro tsarin shiyya-shiyya da ya kebe wa Kudu maso Kudu kujerar Shugaban Jam’iyyar ta kasa. Kuma Tinubu ya karbi wannan tsari ne ba da son ransa ba, saboda ya fi son Cif Bisi Akande ya ci gaba da zama shugaba har abada.
Ya ce hakan ne ya bayar da dama suka tsara sunayen yaransu a matsayin shugabannin jam’iyyar ta kasa.
Ikimi wanda ya fito daga Jihar Edo kamar Cif Odigie-Oyegun, bayan ya caccaki Tinubu, an ce ya rika samun matsi kan ya koma PDP.
Shi kuwa Sanata Olufemi Lanlehin ya fice daga APC ne zuwa AP bayan wata daya da Sanata Ademola Adeseun, da ke wakiltar Oyo ta Tsakiya ya koma PDP daga APC.
Ficerwa sanatocin biyu daga APC ya sauya fasalin siyasar yankin Kudu maso Yamma a daidai lokacin da ake fuskantar zaben 2015. Kuma hakan na iya kawo cikas ga makomar Gwamna Abiola Ajimobi wanda dan APC ne.
Yanzu dai Jam’iyyar APC ba ta da sanata ko daya daga Jihar Oyo, domin sanata na uku Sanata Hosea Agboola, da ke w3akiltar Oyo ta Arewa da ma dan Jam’iyyar PDP ne.
Sauran wadanda suka fice daga APC tare da Sanata Lanlehin sun hada da tsohon Sanata Gbenga Babalola, da shugaban matasan APC, Yemi Aderibigbe