Guguwar Irma manuniya ce kan biranen duniya da ruwa ke kokarin shafe su – Masana

Hadarin da ke tattare da birnin Miami na kasar Amurka shi ne yawan mamayar teku da ke kara karatowa, al’amarin da birnin da wasu biranen duniya ke fama da shi, har ta kai ga ana ganin akwai yiwuwar ruwa ya shafe shi, a cewar masana. Guguwar Irna ta zama manuniya kan biranen duniya da ruwa […]

Guguwar Irma manuniya ce kan biranen duniya da ruwa ke kokarin shafe su – Masana

Hadarin da ke tattare da birnin Miami na kasar Amurka shi ne yawan mamayar teku da ke kara karatowa, al’amarin da birnin da wasu biranen duniya ke fama da shi, har ta kai ga ana ganin akwai yiwuwar ruwa ya shafe shi, a cewar masana.

Guguwar Irna ta zama manuniya kan biranen duniya da ruwa ke kokarin shafe su, domin a karo na farko teku ya yi toroko matuka idan  an kwatanta da daidaituwar kimanin shekaru dubu biyar zuwa dubu shida. Cibiyar Nazari teku ta kasa ta ce torokon teku akwai yiwuwar ya yi ta kara yin sama, kuma mazaunan Miami sun ce yawan ambaliya na aukuwa ne saboda torokon teku a tsawon shekarun nan.

Baya ga nau’ukan hatsabibiyar guguwa da iska da ke kadawa da suka haifar da asara ta wucin gadi, hauhawar torokon teku na bazaranar shafe manyan biranen duniya, wadanda suka hada da Mumbai da Jakarta da Tokyo da Calcuta, a cewar John Englander, ja-gaban kwararru kuma marubuci kan torokon teku ya bayyan a wa Kamfanin Dillancin Labarai na dinhua.

A cewarsa: “Tun daga Washington D.C. zuwa Landan, Ingila birane ne da ke fama da torokon igiyar ruwa, kuma yayin da teku ya yi toroko, wadannan birane na samun yawna ambaliya.”  Bayanan suna kunshe a littafinsa mai taken  Babbar igiyar ruwa a kan babban  titi: Torokon teku mai ankararwar kan matsalar gabar ruwa (High Tide on main Street:  Rising Sea Lebel and the Coming coastal Crisis).

Littafinan kimanta shi a jerin man agartan littafai 50 da shafin sadarwar Amurka mai taken Politico da ya samu karbuwa ya baje.

“A daukacin fadin duniya muna yin gini ne ba tare da la’akari da torokon teku ba.Yanzu teku  ya fara kaimin toroko, don haka sai mun  sake shiri na daban,” inji shi.

Guguwar Irma ta kai farmaki Jihar Florida ta Amurka ranar makon jiya, inda karfin iska  mai cin kilo mita 210 a  kowace sa’a. Wannan guguwa ta tado da ambaliya a titin Miami, kuma ta  yi sanadin katsewar wutar lantarki a gidaje da wuraren kasuwanci sama da miliyan guda da dubu 600.

Kafin karasowarta gabar tekun Florida an fara jin hucinta, inda kalla mutum daya ya mutu, tare da tursasa wata mata ta haihu ba shiri, sannan bishiyoyi da dogwayen gine-gine sun  yi ta lilo a  iska.

Wannan mahaukaciyar guguwa tana cikin mafi karfi da ta taba aukuwa a Atalantika, inda ta halaka mutane 12 a tsibirin Carribean, kuma daga bisani ta doshi kasar Cuba da cin nisan mita 11 a Lahadin. Tsantsarta kadawar guguwar  ta kasance a kwatankwacin mil 50 (kilomita 105) a kudu da Naples da tsakar rana.

Bayan  wucewar wannan guguwa, mutanen da suka kaurace wa gidajen su a Miami sun fara dawowa don gyara muhallinsu.