Guguwar teku mai gudun kilomita 220 cikin awa daya ta tunkari Amurka
Shugaban Amurka, Donald Trump ya ce, gwamnatin kasar a shirye take wajen ba da agajin gaggawa a yayin da guguwar teku ke kara tukarar gabashin kasar. Guguwar tekun da ake yi wa lakabi da Florence, tana da hadarin gaske da kuma karfin maki hudu inda take cin kimanin kilomita 220 cikin awa daya. A safiyar […]

Shugaban Amurka, Donald Trump ya ce, gwamnatin kasar a shirye take wajen ba da agajin gaggawa a yayin da guguwar teku ke kara tukarar gabashin kasar.
Guguwar tekun da ake yi wa lakabi da Florence, tana da hadarin gaske da kuma karfin maki hudu inda take cin kimanin kilomita 220 cikin awa daya.
A safiyar yau Juma’a ce masana suka yi hasashen cewa guguwar ruwan za ta kasance da karfin gaske lokacin da suke ganin za ta iya isa jihohin Karolina da birginia da Maryland da Delaware da kuma Gundumar Kolombiya da suke kan hanyarta.
A ranar Talatar da ta gabata Shugaba Trump ya sa hannu a takardar da ta ayyana jihohin Karolina da birginia a matsayin inda ake da bukatar gaggawa. Lamarin da zai ba da damar kai agajin Gwamnatin Tarayya cikin lokaci.
Akalla sama da mutum miliyan daya ne aka bukaci su tsere daga gidajensu sakamakon munin da ake ganin guguwar da ta nausa take dumfarar gabashin Amurka ke da shi.
Ana kuma ganin cewa guguwar za ta iya watsuwa zuwa wasu sassa na kasar, lamarin da mahukuntan kasar suka yi gargadin cewa kowa ya kasance cikin shirin tunkarar wannan bala’i.
A cikin wani sako da ya aike a shafinsa na twitter, Shugaba Donald Trump ya bayyana guguwar a matsayin daya daga cikin mafiya girma da aka taba gani a Amurka, inda ya bukaci Amurkawa su shirya, su kuma kare kansu.
Shi ma Gwamnan Kudancin Karolina, Henry McMaster ya bukaci mutanen gabashin birnin su kaurace wa gidajensu kafin isowar guguwar a jiya Alhamis, yayin da aka ba da umarnin a rufe makarantu a yankuna 26 daga 46 da ke jihar.