Ana shirin tsige Ganduje daga shugabancin APC
Hotunan Yahaya Bello na neman shugabancin APC sun karade Abuja
Alamomi masu karfi sun bayyana kan yunkurin tsige Shugaban Jam’iyyar APC na Kasa, Abdullahi Ganduje, daga kujerarsa.
Majiyoyi sun ce wasu masu ruwa da tsakin APC daga yankin Arewa ta Tsakiya da na hannun damansu ne suke kokarin raba Ganduje da kujerar domin ta koma yankin.
Wasu rahotanni sun bayyana yadda tsohon Gwamnan Jihar Kogi, Yahaya Bello, yake neman goyon bayan masu ruwa da tsaki domin darewa kan kujerar shugaban jam’iyyar APC.
Hotunan Yahaya Bello na neman shugabancin APC dai sun karade Abuja, awa 48 da saukarsa daga kujerar gwamna, kuma a daidai lokacin da jami’yyar ke shirin gudanar da babban taronta na kasa.
- Ciyamomin Borno za su fara sa hannu a rajistar zuwa aiki
- Amarya da kawayenta sun mutu a hatsarin mota a Neja
A watan Agustan 2023 ne Ganduje, tsohon Gwamnan Kano, ya zama shugaban APC na kasa bayan magabacinsa Sanata Abdullahi Adamu, ya yi murabu.
Abdullahi Adamu ya yi murabu ne sakamakon rikicin cikin gidan jam’iyyar, wanda wasu ke zargin yana da alaka da rashin goyon bayansa ga takarar Shugaba Bola Tinubu a zaben 2023.
Zaman Ganduje shugaban APC abi yi wa masu ruwa da tsakin Arewa ta Tsakiya dadi ba, kasancewar daga yankin Abdullahi Adamu ya fito, don haka suke ganin daga nan ya makata a samu wanda zai karashe wa’adinsa.