Gulak ga PDP: Zan tafi kotu idan aka kwace tikitina
Tsohon Mashwarcin Shugaban kasa kan Harkokin Siyasa Barista Ahmed Gulak ya gargadi Jam’iyyar PDP da kada ta kuskura ta ce za ta sayar da tikitinsa na takarar Sanata ga Gwamnan Jihar Adamawa Barista James Bala Ngilari, inda ya yi barazanar zuwa kotu idan ta yi haka. Barista Gulak ya ce su bakwai suka je Abuja […]
Tsohon Mashwarcin Shugaban kasa kan Harkokin Siyasa Barista Ahmed Gulak ya gargadi Jam’iyyar PDP da kada ta kuskura ta ce za ta sayar da tikitinsa na takarar Sanata ga Gwamnan Jihar Adamawa Barista James Bala Ngilari, inda ya yi barazanar zuwa kotu idan ta yi haka.
Barista Gulak ya ce su bakwai suka je Abuja zaben fidda gwani na sanata a jam’iyyar kuma a lokacin Gwamna Ngilari bai fito takara ba ballantana sayen fom din takarar. “Ngilari bai fito takara ba kuma ko fom bai saya ba, saboda haka ba yadda za a ce shi ne ya ci zaben fidda gwani na mazabar Sanata ta Arewacin Yola,” inji shi.
Ya bayyana wa manema labarai cewa “Ni da wasu mutum shida muka yi zaben fidda gwani na Sanata wato: Kanar Mana da Kari Abubakar da Mista Cliff da Muhammad Murtala da sauransu. Ni na ci zaben fidda gwani na Sanatan Arewacin Adamawa da kuri’a 84 kuma tuni aka bayyana ni a matsayin wanda ya samu nasara kuma an tura sunana zuwa Hukumar INEC. Amma na samu labari a sakatariyarmu cewa za a sauya sunana da na Gwamna, wannan bai dace ba. Don haka zan shigar da kara kotu idan aka yi haka.”
Ya ce Gwamna Ngilari ya zama Gwamna ne yau saboda kotu kuma shi ma zai yi iya kokarinsa har sai ya ci nasara.
Idan ba a manta ba, Gwamna Ngilari ya fadi a zaben fidda gwani na PDP inda Malam Nuhu Ribadu ya sami nasara.