Gulak ya ‘kwace’ shugabancin PDP
Tsohon Mashawarcin tsohon Shugaban kasa Godluck Jonathan kan Harkokin Siyasa Alhaji Ahmed Gulak ya nada kansa a matsayin Shugaban Jam’iyyar PDP ta kasa bayan da ya mamayi hedkwatar jam’iyyar da ke Wadata Plaza a Abuja tare da masu dafa masa baya mutum 10.Yarima Uche Secondus, Mataimakin Shugaban Jam’iyyar PDP ta kasa ne yake rikon jam’iyyar […]
Tsohon Mashawarcin tsohon Shugaban kasa Godluck Jonathan kan Harkokin Siyasa Alhaji Ahmed Gulak ya nada kansa a matsayin Shugaban Jam’iyyar PDP ta kasa bayan da ya mamayi hedkwatar jam’iyyar da ke Wadata Plaza a Abuja tare da masu dafa masa baya mutum 10.
Yarima Uche Secondus, Mataimakin Shugaban Jam’iyyar PDP ta kasa ne yake rikon jam’iyyar bayan da Alhaji Ahmadu Adamu Mu’azu ya yi murabus jim kadan da kada Goodluck Jonathan da Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi a zaven Afrilun bara.
Gulak ya kai karar jam’iyyar wata Babbar Kotun Abuja inda ya bukaci a sauke Secondus daga shugabancin riko yana da’awar cikar wa’adin rikon na wata uku, inda kotun ta ba Secondus mako biyu ya bar kujerar. Sai dai ya daukaka kara zuwa Kotun daukaka kara yana neman a dakatar da aiki da umarnin amma kotun ta ki.
A shekaranjiya Laraba, Gulak ya ce, “Muna nan ne a yau bisa dogaro da hukuncin kotu na ranar 16 ga Disamba, 2015 da kuma hukuncin kotu na yau (ranar Laraba) da ya yi watsi da neman a dakatar da umarnin kotun baya. Kotun a hukuncinta na 16 ga Disamban 2015 ta ce a cikin wuni 14, ni ko wani mutum daga shiyyar Arewa maso Gabas ne za a nada ya maye gurbin Dokta Adamu Mu’azu wanda ya yi murabus daga shugabancin jam’iyyarmu ta kasa a ranar 20 ga Mayun 2015. Bayan cikar kwana 14 a ranar 29 ga Disamban 2015, wanda ake kara ya ki sauka ko ya ki bin umarnin kotu na nada ni ko wani daga Arewa maso Gabas. Kuma bisa aiki da doka da kuma umarnin kotu, yanzu na karvi ragamar shugabancin jam’iyyarmu, musamman da yake a yau (ranar Laraba) kotun ta yi watsi da bukatar dakatar da aiwatar da wancan hukunci,” inji Gulak
Gulak ya ce Babban Kwamitin Jam’iyyar (NWC) ma yana son ya shugabancin jam’iyyar, inda ya ce da ba su so da sun nada wani bayan cikar wa’adin kwana 14 da kotu ta yi umarni.
A karshe ya nada wani kwamitin mutum 11 a karkashin jagorancin Abdullahi Ihioma, wani kwararren akanta ya duba halin da jam’iyyar ciki, inda ya ba shi mako biyu ya mika masa rahotonsa.
Sai dai Mahshawarcin Jam’iyyar kan Harkokin Shari’a, Victor Kwon ya ce jam’iyyar ba ta samu wani bayani kan hukuncin kin dakatar da umarnin kotun farko ba. Mista Kwon wanda ya gana da manema labarai a Legacy House, Abuja, ya bukaci Gulak ya daina sojan gona da tilasta kansa a matsayin shugaban jam’iyyar, ya bari Kwamitin Zartarwa ya zauna don nada wanda ya dace daga Arewa maso Gabas.
Mataimakin Mashawarcin Jam’iyyar kan Harkokin Shari’ar Barista Bashir Maidugu ya ce: “Kotun ba ta mika mukamin ga Gulak ko wani mutum ba. Daga Arewa maso Gabas na fito, idan na ce ina bukatar kuejrar na cancanta.”