Gumsu Abacha: Gwamnan Yobe ya ba da sadakin zinare 24
Gumsu Abacha mai shekara 45 ta zama matar Buni ta hudu.
Gwamnan wanda shi ne Shugaban Riko Jam’iyyar APC na Kasa, ya ba da silallan zinare 24 a matsayin sadakin amaryarsa tasa.
- Ina neman afuwar ’yan Najeriya kan karanci wuta — Ministan Lantarki
- Ina neman afuwar ’yan Najeriya kan karanci wuta — Ministan Lantarki
- Shin yaushe Buhari zai dawo Najeriya daga Landan?
An daura auren ranar Laraba a gidan wan amaryar, Mohammed Abacha ke Abuja.
Daga cikin manyan mutanen da suka halarci daurin auren akwai Shugaban Hukumar Kwastam ta Najeriya, Hameed Ali da babban Kwamishina mai kula da ’yan gudun hijira, Bashir Garba-Lado.
Sauran Mahalartan sun hada da babban malamin Musuluncin, Sheikh Aminu Daurawa da tsohon dan takarar gwamnan Jihar Katsina a zaben shekarar 2019, Yakubu Lado-DanMarke da sauransu.
A shekarar 2019, Buni ya auri ’yar taohon gwamnan Yobe da ya gaji buzunsa, Adama Ibrahim-Gaidam a matsayin matarsa ta uku.
Gumsu Abacha, mai shekaru 45, kafin ta angwance da gwamnan na Yobe, ita ce tsohuwar matar mashahurin me kudin nan dan kasar Kamaru, Bayero Mohamadou.
Sun kwashe kimanin shekaru 20 suna tare da tsohon mijin nata, Bayero Mohamadou, inda igiyar Auren ta datse akarin rabuwarsu a shekarar 2020.