Guragu ’Yan kasuwa na son Ministan Abuja ya samar musu kasuwa
Shugaban gamayyar guragu ’yan kasuwa na birnin Abuja da suka daina bara tuntuni suka rungumi kasuwanci gadan-gadan, Malam Ibrahim Sagir ya roki Ministan Birnin Tarayya Abuja da ya sake tsugunar da su bayan da aka rusa musu kasuwarsu da ke Wuse Zone 3 bayan gidan aikewa da sakonni na NIPOST watanni shida da suka wuce. […]

Shugaban gamayyar guragu ’yan kasuwa na birnin Abuja da suka daina bara tuntuni suka rungumi kasuwanci gadan-gadan, Malam Ibrahim Sagir ya roki Ministan Birnin Tarayya Abuja da ya sake tsugunar da su bayan da aka rusa musu kasuwarsu da ke Wuse Zone 3 bayan gidan aikewa da sakonni na NIPOST watanni shida da suka wuce.
Ya shaida wa Aminiya cewa, ‘kwatsam rana guda aka ce ana gayyatarsu taro da karfe goma na safe, amma da karfe shida na asuba sai hukumar kula da tsarin birnin Abuja, watau Debelopment Control karkashin Hajiya Safiya ta jagoranci rusa musu kasuwar mai mambobi 150 da tebura 80 da shaguna ginannu 20 da rumfuna 6 a filin da tsohon Ministan Ahmad El-Rufai ya basu a 2010.
Malam Ibrahim Sagir ya ce bayan da suka koka sai minista ya gayyace su, inda ya ce zai ba su wuri na dindindin, amma bayan ya tusgunnar da su a shaguna uku a ofisoshin jin dadin al’umma, watau Social Debelopment Center a Area 10. Ya kara da cewa suna koyar da yin takalma da jakunkuna da dinki da kuma gyaran waya.
Malam Ibrahim Sagir ya kuma roki minista da ya shiga tsakaninsu da ma’aikatan banki, wadanda suke damunsu da su biya bashin Naira miliyan bakwai da suka karba.
Ya ce sun biya Naira miliyan biyu saura Naira miliyan biyar kafin a yi musu rusau. Ya roki minista da ya biya musu bashin, sannan ya hanzarta sama musu kasuwa ta guragu don ka da su koma yin bara.