Gurbacewar Bikin Aure A kasar Hausa
Zamani yana zuwa da salo iri-iri da ke yin tasiri ga rayuwar mutane. Al’adar auren Malam Bahaushe na daya daga cikin al’adun da zamani ya riska kuma ya haifar mata da sabon canji da ya saba da abin da aka gada kaka-da-kakanni. MALAM MUDASSIR ALIYU YUNUSA NTA ZARIYA, [email protected] ya yi nazarin al’amarin kuma ya […]
Zamani yana zuwa da salo iri-iri da ke yin tasiri ga rayuwar mutane. Al’adar auren Malam Bahaushe na daya daga cikin al’adun da zamani ya riska kuma ya haifar mata da sabon canji da ya saba da abin da aka gada kaka-da-kakanni. MALAM MUDASSIR ALIYU YUNUSA NTA ZARIYA, [email protected] ya yi nazarin al’amarin kuma ya gabatar da tsokaci kamar haka:
“Abin fahari abin sha’awa al’adunmu ‘yan kasar Hausa. Kyawun asali da tushe a ko’ina an san kasar Hausa…” Kadan ke nan daga cikin baitocin wakar Mai Asayyaro da yake nuni da kuma tabbatar da irin tsari mai kyau na al’adun rayuwar kasar Hausa, wanda tun asali aka san Malam Bahaushe da su. Tabbas haka yake musamman in muka yi duba da irin yadda al’ummomi cikin fadin duniya ke nuna hakilonsu da sha’awarsu dangane da al’adun kasar Hausa.
Biki, bidiri, burede shi ne kirarin da ake wa bikin aure, wanda yana daya daga cikin abubuwa masu matukar muhimmanci a al’adar Hausawa. Akan sanya ranar bikin aure na tsawon lokaci don samun damar shiryawa tsaf don tunkarar bikin. Akan tanadi abubuwa daban-daban da suka hada da kayan abinci, tufafi na ado da kawa da sauran abubuwa na al’ada, domin kece raini da fita kunya.
A bikin aure, iyayen amarya sun fi maida hankali kasancewar su za su wanke, su bayar, shi ya sa shagulgulan bikin suka fi yawa a gidan amare a al’adance, yayin da bangaren amarya suke gudanar da kamun amarya, sa lalle, wunin biki, kafi ko danki, wankan amarya, rakiyar amarya, budar kai, har zuwa ranar da baki za su watse. Su ma dangin angon a nasu bangaren ba a bar su a baya ba, domin akwai shagulgula da suka hada da kamun ango, daurin aure, zaman ajo, cuda, sayen baki da kuma tasani. Haka kuma saboda kawaici, kamun kai da kuma kunyar Malam Bahaushe, dukkan wadannan sabgogin bikin na al’ada ba inda ake cudanya maza da mata sai wajen sayen baki, inda abokan ango da kawayen amarye ke yin rakiya. Wadannan abubuwan su aka fi sani a kasar Hausa wajen gabatar da bikin aure, kodayake a wasu lokutan al’adun sukan sha bamban daga gari zuwa gari a fadin kasar Hausa amma akasari akwai kamanceceniya a bikin Kanawa, Katsinawa, Hadejawa, Zazzagawa, Sakkwatawa da dai sauran garuruwan Hausawa.
Sai dai kash! Abin takaicin a halin yanzu, an gurbata bikin aure a kasar Hausa ta hanyar aron al’adu wadanda ba su da kyau kuma ba su dace da Hausawa ba kwata-kwata, aka gwama su da na Hausawa, a wasu lokutan ma da yawa akan watsar da zubi da tsarin bukin aure na al’ada a dauko na zamani wanda ke cike da rashin kunya da zubar da kima a tsakanin surukai, dangi da kuma maauratan. Abin da ya sa nace haka shi ne, a halin yanzu dabi’ar Turawan yamma ta mamaye bukukuwa a kasar Hausa ta inda tun a farko kafin a kai ga daura aure a lokuta da dama wasu angwaye da amare kan dauki hotuna na rashin kunya da takaici da sunan yin amfani da su a abubuwan da za a raba kyauta a wajen biki, sai ka ga a tsakiyar kasuwa ana yawo da jaka ko wani abu dauke da hoton amarya da ango, ’ya’yan Hausawa cikin fita ko shiga mara mutunci da kamala. Yanzu kam hatta kamun amarya zamani ya gurbata shi, akan gudanar da shi a gwamatse maza da mata, iyaye, ’yan uwa, abokai da kawayen ango da amarya, ana kida ana rawa har ta kai ga uwar amarya za ta iya fitowa ta taka rawa a gaban surukanta da abokansa, har ma su yi mata likin kudi. Haka su ma ango da amarya za a ba su fage don su taka rawa a gaban surukansu.
Tab! Allah wadaran naka ya lalace. Abin da na sani na al’ada dangane da kamun amarya shi ne, amarya kan gudu wani wurin da ba a sani ba, akan kuma sha wahala wajen nemanta gida-gida kafin a gano inda take don a kama ta, amma yanzu kam a bayyane amarya ke zuwa da kafarta wajen da aka tanada don yin kamu cikin taron maza da mata, har wani lokacin ma a yanka kek, ango ya sa wa amarya a bakinta, ita ma ta yanko ta sanya masa a baki wai duk a wajen kamu.
Tirkashi! Me ya kawo dabi’ar Yahudu wan Nasara kasar Hausa? Na san a iya cewa zuwan Turawan mulkin mallaka ne ya kawo irin wannan badakalar, musamman yadda suka nuna fifikon al’aldunsu fiye da namu kuma wai wasunmu suka aminta da hakan; madadin mu yi riko da namu mu kuma nuna musu mun fi su tinkaho da alfahari da al’adunmu na kasar Hausa.
Yanzu har akwai shagulgulan da ake wa lakabi da (European Night, Indian Night Arabian Night da sauransu), inda ake rakashewa da holewa daidai da tarbiyyar jinsin mutanen da aka ambata a wannan daren. Duk da yake wasu al’adun Bahaushe ba su dace da addini ba amma tambayata a nan ita ce, shin da mu da Turawan yamma su waye al’adunsu suka fi cin karo da addinin Musulunci?
Akwai bukatar mu duba zuwa addini da al’adu masu kyau wajen tafiyar da rayuwarmu, musamman wajen gudanar da bukukuwan aure don kada mu rika aiwatar da abubuwan da Allah zai fushi da shi tun a lokacin gudanar da shagulgulansa.
Iyaye na da muhimmiyar gudunmawa wajen guje wa irin wannan tabargazar da ake aikatawa da sunan wayewar zamani. Na tabbata irin sabgogin bikin Hausawa wadanda na ambata a baya suna da matukar tasiri wajen kiyaye mutuncin ma’aurata a tsakanin dangi da abokan arziki, kuma addinin Musulunci wanda Hausawa suka karba ya yi hani da cudanya tsakanin maza da mata don gudun afkuwar wata badalar. Saboda haka tilas ne mu guji dukkan abin da zai kawo debewar albarkar aure.
Allah Ya sa mu ji mu kuma yi watsi da dukkan al’adun banza, musamman irin wadanda Yahudawa da Turawan yamma suke kokarin cusa mana.