Gurbata amfanin gona da cin amana na abokan hulda ya sa na koma noma – Nuhu Beldum

Alhaji Nuhu Beldum, mutum ne da ya jima ya na zagaya wasu kasuwannin amfanin gona a Arewacin Najeriya, inda ya koka a kan yadda baragurbin ’yan kasuwa ke gurbata wasu nau’uka na amfanin gona da nufin samun kazamar riba. Ya kara cewa hakan na gurgunta harkarsu ta hulda da manyan kamfanoni da su ke sayarwa […]

Gurbata amfanin gona da cin amana na abokan hulda ya sa na koma noma – Nuhu Beldum

Alhaji Nuhu Beldum, mutum ne da ya jima ya na zagaya wasu kasuwannin amfanin gona a Arewacin Najeriya, inda ya koka a kan yadda baragurbin ’yan kasuwa ke gurbata wasu nau’uka na amfanin gona da nufin samun kazamar riba. Ya kara cewa hakan na gurgunta harkarsu ta hulda da manyan kamfanoni da su ke sayarwa hajar bayan sun sara daga wajen wasu. Beldum wanda dan asalin garin Girei ne dake Jihar Adamawa, amma ke gudanar da harkar saye da sayar da kayan amfanin gona a Unguwar Kaduna Road dake karamar Hukumar Tafa ta jihar Neja, ya ce a dalilin hasarar da gurbata amfanin gonan ke jawowa, ya sa ya samu raunin gwiwa na cigaba da harkar sannan ya koma noma wasu daga cikin abubuwan da kansa don huce takaici.

Ya ce “Yan kasuwan na gurbata amfanin gona irinsu ridi inda su ke zuba masa yashi mai laushi ko kwallon kashu ta hanyan hada shi da wanda bai kosa ba, ko citta a hadata da mai huna ko mozo ba tare da an zubar da mara kyawu ba. Hakan na jawo mana asara saboda kamfuna na sanya hajar a wajen gwaji, inda na’ura zai nuna adadin mai kyau da na mara kyau a sikile, sannan su biya kudin mai kyau kadai, inji shi. Nuhu Beldum ya ce saye da sayar da amfanin gona ya kai shi garuruwa irinsu: Batsari da Jibiya da Dutsinma a Jihar Katsina, sai kuma Maigatari da Sara da Gujungu da Sakuwa a Jihar Jigawa.

“Haka nan na kan je kasuwannin Mubi da na Yola a Adamawa, da Kumo da Bajoga da Dukku a Jihar Gombe, da Gamawa da Giyade da Gadanmaiwa da Soro a Bauchi, akwai kuma Kachia da Kagarko da Kubacha a jihar Kaduna, sai kuma Funkerewal da Fela da Mamdu a kasar Chadi, da Garoua da Gwom da Adumri da Gwar da Tiboro a kasar Kamaru, sai Tasawa da Maradi a Jamhuriyar Nijar. “Na kan sayi amfanin gona kamar masara da dawa da ridi da waken suya da citta da kwarar kadanya da ’ya’yan kashu da na darbejiya na kaiwa wasu kamfanoni a Lagos, a wani lokaci kuma yaransu ne ke zuwa nan wajen ajiyana su saya, inji shi.

Ya ce a yanzu da ya koma gona ya kan noma: Kabeji da latas da rogo da citta da gyada da kuma rake. “Shi kabeji na kan sayi iri na kanti wanda a ke kawowa daga Faransa na watsa a kan kunya ana yi masa bayi idan a lokacin rani ne sannan ana zuba masa taki, bayan kamar kwana 20 sai a cireshi daga saiwarsa a yi dashensa guda-guda a kan kunya, sannan idan a ka samu karin wasu kwanaki 50 sai a fara girbi a na sayarwa.

“Harkar saye-da sayar da amfanin gona ya taimaka min a rayuwa, a ciki na yi aure na yi gidaje na kuma je haji na sayi wannan gonar tare da kafa makaranta inda a ke karantar da boko da kuma islamiyya. Sai dai dole tasa na ja baya a harkar saboda matsalar ha’inci da cin amana na abokan hulda. “Harka ce da dole sai ka baiwa abokan hulda jarin nemo kaya su na kawo maka kana ba su riba kafin a karshe ka bukaci kudinka. “Sai dai idan ba a yi dace ba sai su yi ta kawo maka kaya marar kyau, idan baka karba ba su kaiwa wani su sayar masa su kara jari, idan ko ka karba kamfani su cire marar kyau a lissafi, sai dai a yi ta yi haka nan idan shekara ta zagayo sai ka dubi wadanda a ka rabu da su lafiya ka kara karfafa hulda da su, wadanda a ka samu matsala kuma ka san yadda za ku wanye, inji Beldum.