Gurbataccen ruwa ya kashe mutum 35 a kauyen Abuja
Kimanin mutum 35 aka hakikance sun rasu sakamakon shan gurbataccen ruwa a kauyen Damagazam da ke Hukumar Birni da Kewayen Abuja (AMAC). Lamarin wanda ya auku a Unguwar Hausawa na kauyen ya fi shafar kananan yara, kuma an fara rasa rayukan ne tun kamar wata shida da suka gabata kamar yadda mai unguwar da lamarin […]
Kimanin mutum 35 aka hakikance sun rasu sakamakon shan gurbataccen ruwa a kauyen Damagazam da ke Hukumar Birni da Kewayen Abuja (AMAC).
Lamarin wanda ya auku a Unguwar Hausawa na kauyen ya fi shafar kananan yara, kuma an fara rasa rayukan ne tun kamar wata shida da suka gabata kamar yadda mai unguwar da lamarin ya faru Malam Abdulhamid Ibrahim ya shaida wa Aminiya.
Mai unguwa Abdulhamid ya ce matsalar da farko tana jawo amai da gudawa zuwa kumburin ciki, sai kuma kisa a mafi yawan lokuta.
Ya ce baya ga mutum 35 da suka rasu, akwai mutum 15 yanzu haka da ke jinya a babban asibitin gwamnati da ke garin Sabo-Wuse ta Jihar Neja, inda binciken likitoci ya nuna cewa matsalar ta zazzabin taifod ne, inji shi.
Mai unguwar ya ce al’ummarsu sun gwammace zuwa wancan asibitin ne duk da cewa ba ya yankin Abuja saboda ya fi saukin jinya. “Sai dai akwai wadansu kalilan da ke jinya a asibitin Kabusa, sai kuma ’yata Hassana da wata baiwar Allah ta dauki nauyin jinyarta a Asibitin Asokoro da ke Abuja bayan ’yar uwarta Husaina ta rasu a Asibitin Sabo-Wuse,” inji shi.
Ya ce da farko suna sayen magunguna ne a wurin masu talla da kemis ga yaran da suka kamu da cutar, kafin a kai ga asibiti idan ciki ya kumbura.
Wata malamar jinya a sashin kula da yara na asibitin Asokoro inda aka kai yarinyar, ta shaida wa wakilinmu cewa yarinyar na fama ne da zazzabin taifod wanda ta ce na faruwa ne sakamakon shan gurbataccen ruwa ko abinci mara tsabta.
Malamar jinyar wadda ta nemi a sakaya sunanta ta ce an yi wa yarinyar aiki a hanjinta har sau biyu saboda yana tsinkewa kuma shi ne ke haddasa kumburin cikin, ba tare da samun cikakken nasara ba, saboda haka ta ce za a sake yi mata aiki na uku.
Wani dan siyasa a kauyen mai suna Malam Idris Abdullahi ya ce “A makon jiya ne a yayin taron mazaba da ya gudana a yankin Durumi na sanar da shugabannin jam’iyyarmu cewa su taimaka mana da addu’a annoba ta barke a kauyenmu. Bayan sun ba mu shawara ne sai mai unguwa ya aika da dansa zuwa ofishin kiwon lafiya na Abuja suka zo suka taimaka mana da magunguna da kuma yin gwaje-gwaje a rijiyoyinmu da wani wurin da muke dibar ruwa da mu ke dibar ruwa. “
Jama’ar kauyen sun ce da farko ba su san musabbabin mace-macen ba sai bayan zuwan jami’an kiwon lafiya ne suka shaida musu cewa matsalarsu, ta shan gurbataccen ruwa ne, saboda haka sun bukaci Hukumar AMAC taimaka musu da rijiyar burtsatse inda suka ce guda biyu da ke wurin na tuka-tuka ne da wata kungiyar Kirista da kuma wata baiwar Allah suka yi musu kuma tuni suka daina aiki.
Babban Sakataren Hukumar Kula da Lafiya a Matakin Farko na Abuja, Dokta Rilwanu Muhammad wanda ya jagoranci jami’an kiwon lafiya zuwa kauyen a ranar Asabar da ta gabata, ya ce sai a ranar 4 ga Agustan nan ne Mai unguwar ya aike da dansa ofishinsu don sanar da su lamarin “Kuma sakamakon haka muka kai ziyarar gaggawa tare da ba su magunguna da fadakar da su a kan cutar. Mun kuma dauki samfurin ruwan da suke amfani da shi a rijiyoyi da rafi don yin gwaji bayan mun aiwatar da gwaji a kan ’ya’yansu. Akwai kuma shirin kafa tanti a yankin don ci gaba da kula da su,” inji shi.