Gurgu mai hawan gado da kyar ya hau saman ‘Burj Khalifa’ gini mafi tsawo a duniya

Burj Khalifa shi ne ginin mafi tsawo a duniya

Gurgu mai hawan gado da kyar ya hau saman ‘Burj Khalifa’ gini mafi tsawo a duniya

Ginin Burj Khalifa

“Ina fafutika wajen hawa gadona saboda gajarta da nakasa amma a yau na hau gini mafi tsawo a duniya,” inji wani wada wanda yake alfahari da haka mai suna Alif Mohammed yayin da ya samu nasarar hawa gini mafi tsawo a duniya na ‘Burj Khalifa’ da ke birnin Dubai a Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE), a balaguron farko da ya yi zuwa kasashen waje.

Alif dan kasar Indiya mai shekara 20 duk lokacin da ya tafi yawon bude-idon yakan yi amfani da taimakon abokan karatunsa Aarya da Archana don fita wani wuri, kuma wannan balaguro bai bambanta ba da sauran ba da sauran.

Mafarkin Alif ya zama gaskiya lokacin da shi da abokan nasa biyu suka samu kansu a ginin ‘Burj Khalifa.’ Sun ji dadin ganin gari daga saman ginin.

Bayan faifan bidiyo na masu ziyarar su ukun ya fara yaduwa a farkon bana, wata Hukumar Balaguro da ke Dubai ta yanke shawarar taimakawa wa tafiyar matasan, tare da rakiyar mahaifiyar Alif, zuwa cikin birnin don kai su hutun da ba za su taba mantawa ba.

A cikin watan Maris din bana ne a lokacin wani bikin al’adu a kwalejinsu Alif, wanda aka haifa da lankwasasshiyar kafa, abokan karatunsa Aarya da Archana suka kai shi harabar makarantarsu. Ga bakin uku, wannan ba wani abu ba ne na yau da kullun.

Kusan kowane abokin karatunsu na rukunin 70 a Kwalejin DB a Shasthamkotta a Kerala sun taimaka wajen daukar Alif yawon bude-ido. Duk da haka, lokacin da Alif ya wallafa wannan bidiyo a shafinsa na Instagram, ya samu daukar hankalin mabiyansa cikin sauri.

Kafofin watsa labarai sun nuna matukar so da nishadi kan bidiyon da ya wallafa. Daga baya, yayin da yake tattaunawa da wani gidan rediyo da ke Dubai a harshen Malayalam, Alif ya ce burinsa ne a tsawon rayuwa ya ziyarci Dubai.

“Lokacin da na ji haka, na san dole ne in kawo shi ya ga Dubai,” inji Afi Ahmed, Manajan Darakta na Hukumar Balaguro ta Smart Trabel, da suka yi rakiyarsa a jirgi cikin ayarinsu a kan duk fitarsu.

“Ina ganin ya kamata a yi bikin kyawawan ayyuka. Wannan ita ce, hanya daya da za a kiyaye dan Adam da zaburar da mutane da yawa don yin nagarta.

“Duk yara mazan da ke kwalejin suna son su dauke shi, amma kawai yana son ’yan matan kwalejin su yi haka,” Aarya ta tsokani Alif, yayin da Archana ta yi dariya.

Dukkansu uku sun kammala karatun digiri na farko a fannin kasuwanci.