Gurgu mai lalata da yara mata ya shiga hannu a Kebbi
Wani gurgu da ake zargin ya dade yana bata kananan yara mata ya shiga hannun jami’an tsaro a Birnin Kebbi. Gurgun mai suna Abdul’aziz Mohammed wanda aka fi sani da suna Soshiyal mai kimanin shekara 50, an ce yana sana’ar sayar da filaye ne, kuma yana zaune ne a Unguwar Badariya a Birnin Kebbi. Ana […]

Wani gurgu da ake zargin ya dade yana bata kananan yara mata ya shiga hannun jami’an tsaro a Birnin Kebbi.
Gurgun mai suna Abdul’aziz Mohammed wanda aka fi sani da suna Soshiyal mai kimanin shekara 50, an ce yana sana’ar sayar da filaye ne, kuma yana zaune ne a Unguwar Badariya a Birnin Kebbi.
Ana zargin gurgun ne da lalata da wadansu yara mata ne uku da shekarunsu suka kama daga takwas zuwa 11.
Aminiya ta tattauna da gurgun bayan ya shiga hannun jami’an tsaro, inda ya ce idan yaran sun fito talla suna biyowa ta dakinsa sai ya saye kayan tallar kuma ya kara musu kudi domin su yarda da shi, shi kuma sai ya yi amfani da wannan wajen lalata da su, amma ba a lokaci daya suke zuwa ba, sukan zo ne lokuta daban-daban.
Ya ce ya dauki tsawon lokaci yana lalata da yaran har zuwa lokacin da dubunsa ta cika. Ya ce yana da matar aure daya da ’ya’ya uku, inda ya danganta aukuwar hakan da aikin Shaidan.
Wadansu mutanen unguwa sun dora alhakin aukuwar hakan a kan rashin kula da kuma sakacin iyaye masu dora wa ’ya’yansu talla.
Hakimin Badariya Alhaji Mohammed Abdullahi wanda ya nuna bacin ransa a kan aukuwar wannan abu, ya ce za su dauki matakin da ya dace tare da masu unguwanni wajen sa ido a kan miyagun mutane da suke cikin jama’a. Ya gargadi iyayen yara su kula tare da sa ido a kan amanar ’ya’yan da Allah Ya ba su.
Kwamandan ’Yan banga na Jihar Kebbi, Alhaji Lawali Augie ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce wanda ake zargin ya tabbatar da zargin da ake yi masa na bata yaran. Kuma a binciken da suka yi sun samu wanda ake zargin da bata wata jikar ’yar maigidan da yake zaune a gidansa kuma an koro shi daga garin Jega ne saboda irin wannan aika-aika ta lalata da kananan yara mata, inda ya dawo Birnin Kebbi. Ya ce suna shirye-shiryen gabatar da shi a gaban kotu da zarar sun kammala bincike.