Gurgu ya mike a ranar daura aurensa

Wani sabon ango mai suna Kebin Taylor a kasar Amurka, wanda ya samu karaya tsawon shekara 13, ya mike a ranar daurin auren sa, inda amarya ta yi kukan dadi.Mista Kebin ya yi fama da cutar daurewar jijiya baya ga karayar da ya samu shekara 13, inda al’amari ya bayyana karara a shekarar 2009, kamar […]

Gurgu ya mike a ranar daura aurensa
Gurgu ya mike a ranar daura aurensa

Wani sabon ango mai suna Kebin Taylor a kasar Amurka, wanda ya samu karaya tsawon shekara 13, ya mike a ranar daurin auren sa, inda amarya ta yi kukan dadi.
Mista Kebin ya yi fama da cutar daurewar jijiya baya ga karayar da ya samu shekara 13, inda al’amari ya bayyana karara a shekarar 2009, kamar yadda likitansa ya nuna cewa, lallai akwai bukatar a yanke kafar. Abokansa kuwa suna yaba wa irin kwarin gwiwarsa, musamman ganin cewa, bnai cika kokawa da halin da yake ciki ba.
Kwatsam sai rayuwarsa ta sauya Wannan mata ’yar asalin jihar Tedas ta amince ta auri Kebin duk da kasancewarsa gurgu, da aka sanya ranar bikin aure, bayan an gayyaci abokan arziki da ’yan uwa, sai Kebin ya gwada tashi tsaye da yin tafiya. Kebin Taylor ya yi aiki tukuru wajen yin tafiya na tsawon makonni har ma watanni, inda ya rika shafe sa’o’i yana kwatanta yin tafiya.
Da aka zo wurin daurin aure kafin a fara biki, daukacin baki duk sun zauna, sai mahaifin amarya ya shigo da ’yarsa. Da limamin majami’a ya tashi, sai ya umarci daukacin mutanen da suka halarci taron da cewa, “kow aya tashi tsaye.” Shi ma Kebin Taylor sai kawai ya mike. Da ganin haka sai amarya ta kama kukan dadi, har ma ta kasa cewa komai. Sabanin yadda ta saba ganin saurayinta wanda ya zama amngonta a wannan ranar, da akan keken guragu, yau kuma ga shi tsaye.
Wannan farin ciki na amarya ya wuce kimantawa. Kafar sadarwa ta www.healthadbisorgroup.com ta baza labarin a duniya.