Gurgun da ke bara dauke da Naira miliyan 37 a aljihunsa

An kama mutumin ne da kudin a cikin kafarsa ta roba

Gurgun da ke bara dauke da Naira miliyan 37 a aljihunsa

Wani gurgu ya fada hannun ’yan sanda sakamakon kama shi da aka yi yana bara dauke da tsabar kudi Dala 81,000 (kimanin Naira miliyon 37.3) a cikin kafafun robar da yake tafiya da su.

Gurgun dai, wanda da aka yanke wa kafa, kuma yake tafiya da kafar roba da taimakon sandar guragu an kama shi ne a birnin Dubai na Hadaddiyar Daular Larabawa.

Mutumin wanda ba a bayyana sunansa ba da kuma kasar da ya fito, ya fada hannun ’yan sanda ne bisa shiga kasar da takardar biza ta ziyara.

An kama shi ne a ranar Alhamis 16 din da ta gabata, yana bara a masallatai da wuraren shakatawa kamar yadda jaridar Gulf News ta rawaito.

’Yan sandan suna zargin mabaracin gurgun da yin karya, kasancewar an samu tarin kudin boye a cikin kafarsa ta roba duk da yake yana nuna cewa shi mubukaci ne da ke neman taimakon jama’a.

Rundunar ’Yan sandan Dubai da ta yi kamun ta gargadi jama’a da kada su rudu da mabarata da suke kirkirar dabaru daban-daban don neman tausayawarsu.

Babu sojojin ƙasar waje a yankinmu —Sakkwatawa

Yadda dagacinmu ya sassara ni da adda — Maraya

Bidiyoyin da suka ɗauki hankalin ’yan Najeriya a 2024

An kama mutum 859 da ceto 46 da aka yi garkuwa da su a Filato – ’Yan sanda