Gurguwar Dabara
Gwamnatin Shugaba Muhamadu Buhari ta sha daukar matakan yin kwaskwarimar da za su inganta matsayi da kuma kyautata ayyukan hukumar mai ta kasa da ake kira NNPC, an kuma dauki matakan binciko abubuwan da ke kawo mata cikas ko hana ruwa gudu, amma sai ga shi nan har yanzu babbar matsalar da ake kuka da […]
Gwamnatin Shugaba Muhamadu Buhari ta sha daukar matakan yin kwaskwarimar da za su inganta matsayi da kuma kyautata ayyukan hukumar mai ta kasa da ake kira NNPC, an kuma dauki matakan binciko abubuwan da ke kawo mata cikas ko hana ruwa gudu, amma sai ga shi nan har yanzu babbar matsalar da ake kuka da ita, wacce kuma ta yi sanadiyyar daukar wadancan matakan kawar da su tana nan ba ta kau ba, jama’a kuma na ci gaba da fama da irin matsalolin da take haddasawa. Dangane da haka ana iya cewa, ita dai wanan hukumar ta NNPC ta kasa gano dabarun shawo kan matsalolin da ke addabarta shekaru aru-aru, musamman wajen samar da man da motoci, manya da kanana ke amfani da shi cikin saukI, idan aka yi la’akari da yadda ta dukufa wajen giggina manya-manyan gidajen sayar da man na kashin kanta, yayin da gidajen mai ke zamantowa fankam-fayau babu man da jama’a ke dogayen layi a gabansu don su saya.
Abin da wannan al’amari na kara yawan manyan gidajen mai da ake kira Mega Stations da hukumar NNPC ke yi yake nunawa a halin yanzu, musamman ma a wannan lokacin da Gwamnatin tarayya ba ta ce komai ba game da manufarta na farfado da matatun man kasar nan guda hudu da suka kwanta da siradansu, shi ne kokarin magance karancin man fetur ga masu tsananin bukatarsa ta hanyar kara yawan wuraren sayar da shi. To, a bisa gaskiya ba haka nan zancen yake ba, duk kuwa da cewa manyan jami’an hukumar NNPC sun yi amanna da cewa, giggina manyan gidajen man da hukumarsu ke yi ne kadai mafita daga magance tasgaron da aka dade ana fuskanta wajen samarwa da kuma rarraba man fetur da na dizal, har ma da kananzir a dukkan wuraren da ake amfani da su.
A cewar manya-manyan daraktocin hukumar, burin su, shi ne, giggina irin wadanan manyan gidajen sayar da man guda uku-uku a kowace jiha, watau guda daidai a kowace mazabar dan majalisar dattijai, inda daga karshe za a samar da gidajen mai guda dari da tara a fadin tarayyar kasar nan. E, to, an ji cewa, za a samar da wadannan gidajen man, amma ai ba a nan take ba, wai an danne bodari a kai. Samar da gidajen mai barkatai haka, ba shi ne maganin wannan matsalar ba, domin kuwa ba sai man ya wadatu ba ne sa’anan za a kai shi gidajen da aka giggina don sayarwa ba, ko kuwa mutum na iya sayar da abin da ba shi da shi, a shagunan da ya giggina a gidansa?. Kamata dai ya yi hukumar NNPC ta bar batun samar da wuraren sayar da mai don magance karancinsa ga ‘yan kasuwa da kamfanonin da ke sha’awar yin haka, domin kuwa wannan aiki ba nata ba ne. A wasu kasashen da suka bayar da muhimancin dillancin albarkatun man fetur, kamfanoni kamar su NNPC sun fi mayar da hankulansu ga yadda za a sarrafa albarkatun man fetur da dangoginsa. Sai idan har gwamnati ta gano cewa ‘yan kasuwa da kamfanoninsu na son yi mata zagon-kasa ne game da haka za ta dauki matakan hukunta su, ko kuma wargaza tsarinsu don kada ya yi tasiri.
An dai kiyasta cewa a Najeriya akan kona man fetur sama da lita miliyan 40 a kullum, kuma idan har matatun man kasar nan guda suka kama aiki yadda ya kamata, sukan fitar da lita miliyan goma a kullum, watau ke nan hakan na sa ana samun gibin lita miliyan 30 ke nan wadanda za a bukaci shigowa da su kasar nan a kullum. To amma a ‘yan shekarun baya, sa’ilin da matatun man kasar nan guda hudu, suka kwanta dama, ba su samar da komai don rage yawan man da ake sayowa daga kasashen ketare.
To a bisa gaskiya a nan ne fa gizo ke sakar, kuma dangane da haka an fahimci cewa rumfuna ba u ne kasuwa ba, abin da za a sayar ne a cikinsu mafi muhimmanmci. Ashe ke nan kara yawan mayan gidajen sayar da man fetur da NNPC ke kokarin yi ba zai magance matsalar karancin mai ba, domin kuwa sai an samar da shi ne a nan cikin gida, ko an yi sautunsa daga kasashen ketare za a kai can, a sayar.
A wannan marrar da man fetur ke wahalar samu fiye da ruwan Bagaja, hatta gidajen mai na Mega da hukumar NNPC ke samarwa, suna ba jama’ar da suka je neman mai hakuri, saboda su ma ba su da shi. To yaya ke nan? Yaya kuwa in ban da kawai a inganta hanyoyi da dabarun samun man da za a sayar a gidajen mega? Hakan shi ne mafi a’ala a wannan marrar da gwamnatin canji ke da’awar kawar da tallafin farashin man fetur. To ai ko da ma can tsarin shigo da man fetur daga ketare ne ya kawo batun tallafin farashin don talakawa su samu da sauki. Wannan ne ya kai Najeriya gwada hali irin na bakauyen da zai kai danyen rogo kasuwar birni, bayan ya sayar zai koma gida sai ya sayi dafaffen rogon, ya tafi da shi kauye.
To, muddin dai gwamnati na sha’awa da bukatar samar da man fetur a farashi mai rangwame sosai, to fa wajibi ne ta dukufa wajen samar da shi a nan cikin gida, kuma yadda zai wadatu a ko ina. Ta haka ne za a daina tsawwala farashinsa a dukkan lokutan da farashin danyen mai ya fara cillawa sama a kasuwannin duniya. A cikin ‘yan watani da hawanta, Gwamnatin Shugaba Buhari ta ce ta bayar da lasisi ga masu sha’awar kakkafa kananan matatun mai a nan cikin gida har guda 34, amma tun bayan sanarwa game da haka, ba a sake jin komai ba game da batun su, ko kuma game da niyyar gwamnati na farfado da matatun da ake da su.
Watanni takwas a rayuwar gwamnatin da za ta yi shekaru hudu ba kwanaki takwas ne ba, kuma ya kamata a ce a cikin wadanan watannin an gama farfado da matatun man kasar nan, an kuma kammala dukkan tsare-tsaren da aka yi niyyar yi don inganta matsayin hukumar mai ta NNPC, an kuma kawar da dukkan matsalolin da suka durkusar da ita tun can farko. ‘Yan Najeriya dai sun kosa su fahimci irin shirye-shiryen da gwamnatinsu ke yi dangane da haka, ta kuma fayyace musu abubuwan da ya kai ta ga jan-kafa a wadannan fannonin. Ai ko ba komai ya kamata ta yi haka, domin korafin jama’a ya fara yin yawa game da yadda gwamnati ta dukufa wajen giggina gidajen mai na “Mega station,” maimakon farfado da matatun mai. Wannan abin dai shi ake kira gurguwar dabara ko kuma baya ba zani.