Gurguwar Likita ta shekara 15 tana kula da marasa lafiya
Wata mata mai gundulmin kafa da aka datse mata a sanadiyyar hadarin mota, ta zama likitiyar da ke kula da mazaunan karkara mutum dubu. A yankunan tsaunukan Kudu maso Yammacin kasar Sin, da ke karkashin birnin Chongking.Li Hongju ’yar shekara 37, ta lalata kananan kujerun mata 24, lokaci8n da take aikin likitanci, inda aka rika […]
Wata mata mai gundulmin kafa da aka datse mata a sanadiyyar hadarin mota, ta zama likitiyar da ke kula da mazaunan karkara mutum dubu. A yankunan tsaunukan Kudu maso Yammacin kasar Sin, da ke karkashin birnin Chongking.
Li Hongju ’yar shekara 37, ta lalata kananan kujerun mata 24, lokaci8n da take aikin likitanci, inda aka rika kiranta wajen kula da majinyata har sau dubu shida, tsawon shekara 15.
Da rana cikin watan Maris din shekarar 1983, Li Hongju ’yar shekara hudu na kan hanyarta ta zuwa makarantar, sai wata babbar mota ta ture ta, ta kuma makale a karkashin motar. Bayan an datse mata kafafuwa, abin da aka rage bai wuce tsawon sentimita uku ba.
Lokacin da ta kai shekara takwas, sai ta koyi yin tafiya, ta hanyar dogara hannayenta da amfani da kujerar mata. Saboda tsananin wahalar ciwo da ta sha, sai Li Juhong ta dcauri aniyar zama likita, don ceto rayuwar mutane.