Guzirin Ma’aurata Don Ramadan 2

Assalamu alaikum; barkanmu da sake haduwa cikin wannan fili, da fatan Allah ya amfanar da mu dukkan bayanan da za su zo cikinsa, amin. Ga ci gaban bayani kan tanade-tanade, da shirye-shiryen da ya kamata ma’aurata su yi don tarbar wata mai alfarma na Ramadan, da fatan Allah ya sa wannan bayani ya isa ga […]

Guzirin Ma’aurata Don Ramadan 2
Guzirin Ma’aurata Don Ramadan 2

Assalamu alaikum; barkanmu da sake haduwa cikin wannan fili, da fatan Allah ya amfanar da mu dukkan bayanan da za su zo cikinsa, amin. Ga ci gaban bayani kan tanade-tanade, da shirye-shiryen da ya kamata ma’aurata su yi don tarbar wata mai alfarma na Ramadan, da fatan Allah ya sa wannan bayani ya isa ga duk masu bukatarsa, kuma ya amfanar da su, amin.

Guziri Na 3: Gyara Da Shirya Muhalli: Babban bako, mai matukar muhimmanci zai bakunci gidanku ya ku ma’aurata; don haka yana da matukar muhimmanci ku yi dukkan shiri da ya kamata don yi masa tarba mai kyau da ba shi mafi kyawun masauki a cikin gidanku. Don tabbatar da haka, sai ku yi amfani da wadannan hanyoyi:
Kwana biyu ko uku kafin Ramadan, sai a share gida gaba dayansa, a cire yana, a kwashe kwata; a rage tarkace, mai sauran amfani a kyautar ga masu bukata, marasa amfani a zubar a bola.Sannan a rage like-like da kayan kawa, musamman hotuna da like-liken kwalliya masu daukar hankali lokacin ibada; sannan a gyara wuraren da siminti ya farfashe musamman in ruwa na yawan taruwa a wurin; in kuma fentin gidan ya tsufa, kuma inda akwai halin yin sabo to sai a yi ga duka ko wani bangare mafi muhimmanci na gidan.
A tanadi hanyar samun ruwan amfanin yau da kullum, in wani fanfo na bukatar gyara, ko rijiya na bukatar yasa, duk sai a yi kokarin a yi su kafin Ramadan.
A tanadi hanyoyin samun haske da daddare, canza kwan lantarkin da ya mutu, tanadar fitila mai amfani da batiri, masu halin janareta su tabbatar da lafiyarsa, kuma su yi masa duk tanadin da ya kamata kafin Ramadan.
A tabbatar cewa murhun da ake amfani da shi, na itace, risho ko na gas, bai da wata matsala, in kuma yana da matsala a yi kokarin gyarawa kafin Ramadan. Sannan a tanadi makamashin konawa, watau itace, kalanzir ko gas daidai gwargwadon hali.
A tanadi dukkan kayan abinci daidai gwargwadon hali, sannan masu bukatar gyara sai a gyara su yadda da an zo amfani da su cikin Ramadan, kawai sai dai a sarrafa ba sai an tsaya gyarawa ba.
A yi dukkan saye-sayen kayan Sallah, da dinkunan Sallah tun kafin Ramadan, ta yadda in watan ya tsaya sai dai a maida hankali wajen ibada da bautar Allah kadai.
A kaurace ma kallon talabijin ko sauraren kade-kade, sai na shirye-shiryen addini kadai; in kuma har ya kasance garin kallonsu za a kunno wasu tashoshin wasannin banza, to sai a dauke talabijin din gaba daya daga wajen kallon har sai bayan Ramadan.
Guziri Na 4: Jadawalin Ramadan: Lokaci abu ne mai matukar muhimmanci a rayuwar bil’adama, rashin sarrafa shi yadda ya kamata na jawo ma dan’adam asara mai yawa da kuma ci baya a rayuwarsa. Don haka duk mai son ya ribaci dukkan alheran da ke cikin watan Ramadan, dole sai ya tsara, ya kuma shirya lokacinsa ta hanyar yin abubuwan da suka dace a lokacin da suka dace. Abin da zai taimaka wa mutum cimma wannan shi ne ta hanyar yin jadawalin lokacinsa. Yin jadawali da amfani da shi abu ne mai matukar muhimmanci kuma mai tabbatar da cin nasara cikin rayuwa.Mu duba makarantu da manyan kamfanoni, amfani da jadawali shi ke dawwamar da kasantuwarsu, inda ba su aiki da jadawali, cikin karamin lokaci zas u samu matsala.
Yadda za a tsara Jadawalin Ramadan: Don samun sauki wajen tsarawa, sai ma’aurata su tsara ayyukan da suke son aiwatarwa a rana a cikin sa’o’in da ke tsakanin lokacin sallolin farilla biyar; misali, sai a fara da ayyukan da ake son aiwatarwa a lokacin sahur, bayan Sallar Asuba kafin Sallar Azahar; bayan Azahar kafin la’asar; bayan la’asar kafin magriba; bayan magriba kafin isha’i; bayan isha’i da tarawiy kafin lokacin sahur; sai a bi a cike wadannan lokuta da ayyukan da suka dace, kuma ana fara sa aikin da ya fi muhimmanci, ko wanda yake dole, sannan mai bi masa a muhimmanci, sannan mai bi masa har a hada duka. Tunda ba komi ne ma’aurata ke yi tare ba, kuma ba koda yaushe suke tare ba, ya kamata ma’aurata ya kasance kowa yana da jadawalinsa, sannan kuma su yi wani na gida guda daya wanda zai kunshi kowa da kowa har yara duka. Don ganin alfanun dake cikin yin jadawalin lokaci, DOLE sai ma’aurata sun ladabtar da kansu ga yin amfani da shi yadda yake, ba tare da tsallake wani aiki ba ko daukar aikin wani lokaci a kai shi wani lokaci, kuma dole su ladabtar da dukkan wadanda ke karkashinsu wajen yin aiki da jadawalin nan sau da kafa.
Guziri Na 5 Gyara Dangantaka: Ma’aurata, yana da kyau ku yi dukkan kokari na gyara da inganta dangantakarku kafin isowar watan Ramadan, da hakane za ku dace da cin ribar dukkan alheran da ke cikinsa. Ku yi kokarin kara kusanci da shakuwa da juna, da kuma kara karfafa zumuncin auren da ke tsakaninku. karin kyautatawa ga juna, karin yin hakuri da juna, da sauran kyawawan abubuwa na dadada ma juna. Ku zauna ku tattauna game da dangantakarku, ku yi afuwa ga juna, ku toshe duk wata baraka da ke tsakaninku don ya kasance in Ramadan yazo, ba abinda ke gabanku sai more rahmar da ke cikinsa da yin ibada.
Sai sati na gaba insha Allah, da fatan Allah ya sa mu kasance cikin kulawarsa a koda yaushe, amin.f