Guzuri ga Maniyyata aikin Hajji

Ya kai dan’uwana Alhaji, wanda Allah Ya zabe shi a tsakanin miliyoyin Musulmi, domin ziyarar dakinSa mai alfarma, ina rokon Allah da ya jibinci al’amuranka a Duniya da Lahira, kuma ya sanya ka mai albarka duk inda kake.Ya kai dan’uwa mai girma, ya kai wanda ka gamu da wahalhalun tafiya, kuma kayi hakuri da su, […]

Guzuri ga Maniyyata aikin Hajji
Guzuri ga Maniyyata aikin Hajji

Ya kai dan’uwana Alhaji, wanda Allah Ya zabe shi a tsakanin miliyoyin Musulmi, domin ziyarar dakinSa mai alfarma, ina rokon Allah da ya jibinci al’amuranka a Duniya da Lahira, kuma ya sanya ka mai albarka duk inda kake.
Ya kai dan’uwa mai girma, ya kai wanda ka gamu da wahalhalun tafiya, kuma kayi hakuri da su, kuma ka fitar da dukiyarka, kuma ka bar gidanka, ka yi bankwana da iyalinka da ‘ya’yanka, ba don komai ba sai domin sauke faralin da Allah ya dora maka, na ziyarar dakinSa mai alfarma, Allah ya sanya hajjinka karbabbe ne, kuma ya gafarta maka zunubanka, ya rufa maka asiri tare da mu gaba daya.
Ya dan’uwana Alhaji, saboda son da nake maka da sha’awar da kake ba ni, tare da farin cikina da zuwanka, da jin dadina da kubutarka, ya sa na fuskance ka da wasu sakonni, saboda in sauke wani wajibi da ya hau kaina, game da kai, kuma in kasance na bi umurnin Allah da ya ce: “Kuma suka yi wa juna wasiyya da gaskiya, kuma suka yi wasiyya da hakuri”.(asr 3)
Kuma in bi umurnin masoyinmu, shugabanmu, abin koyinmu, Annabinmu Muhammad (SAW) da yake cewa: “Misalin Muminai wurin soyayyarsu da jin kan junansu, da suke yi, kamar misalin jiki daya ne, idan wata gaba ta kamu da cuta, sai sauran jikin ya kamu da zazzabi da rashin barci”. Manzon Allah (SAW) ya sake cewa: “Mumini ga dan uwansa mumini, kamar gini ne sashinsa ne ke karfafa sashi”.
dan’uwana Alhaji, kar ka manta da abin da ya kawo ka wannan gari, wato hajji, ka sani cewa shi hajji da ma sauran ayyuka baki daya, Allah ba ya karba, sai aikin ya zama domin shi a ka yi, da haka ne za ka samu ladan aikin, Allah yana cewa:
“Kuma ba a umurce su da kome ba, face su bauta wa Allah, suna masu tsarkake addini gare shi, suna masu karkata zuwa addini gaskiya…” (bayyinah 5)
Kuma kafin a karbi aiki dole ne ya zama an yi aikin daidai, bisa sunnar Manzon Allah (S.A.W), Manzon Allah (S.A.W) yana cewa: “Duk wanda ya aikata wani aiki (don kansa) ba tare da umurninmu ba, to an mayar masa da aikinsa.”
Ya kamata tunaninka kullum ya kasance: Shin an karbi aikinka ko ko a’a?
Maganar aikin hajji kuwa Manzon Allah (S.A.W) yana cewa: “Ku koyi aikin hajjinku a wurina”. Wato duk abin da na yi a cikin aikin hajji to kuma ku yi irin sa, kada ku kago wani abu daga wurin ku.
Aikin hajji mafi kyau da Musulmi zai yi, shi ne ya yi shi yadda Manzon Allah (SAW) ya koyar, don ya yi katari da soyayya daga Allah tare da gafararSa. Allah yana cewa:
“Ka ce: idan kun kasance kuna son Allah, to ku bi ni, Allah zai so ku, kuma ya gafarta muku zunubbanku”. (Al Imran 31)
Saboda haka ya wajaba a kanka – ya kai dan uwa Alhaji – ka koyi hukunce-hukuncen aikin hajji, kuma ka tambayi malamai kafin ka fara, domin ka yi dace da sakamako mai kyau a wurin Allah.
Haka zalika Shugaban ya ja hankalin mahajjata da cewa Su kula sosai yayin zaman su a birnin Makkah da Madina, domin Falalar da ke cikin sallah a masallachin Makka da Madina, a duk lokacin da ka tsinci kanka a wadannan wurare.
Allah Madaukakin sarki yana cewa a cikin Alkurani maigirma, “LALLAI dAKIN BAUTA NA FARKO WANDA ALLAH YA SANYA SHI GA MUTANE DON BAUTA SHI NE, WADDA YAKE GARIN MAKKA MAI ALBARKA A KUMA SHIRIYACE GA DUKKAN HALITTU, CIKINSA  AKWAI AYOYI BAYYANANU…… (suratu Aliimran 96-97). Kamar su makama Ibrahim , Hajarul aswad, dutsen Safa da Marwa, ruwan Zamzam. Wadannan duk a bayyane suke, kuma dukkan Masallatan Duniya babu inda za ka je ka samu wadannan sai masallacin Haram na Makkah.
An karbo hadisi daga Jabir dan Abdullah Allah ya kara masa yarda yache Annabi (S.A.W) ya ce: SALLAH A CIKIN WANNAN MASALLACINA  (MASALLACIN MADINA), YA FI SALLAH DUBU A CIKIN WANI MASALLACIN DA BASHI BA, SAI DAI MASALLACIN MAKKA, (MASALLACIN KA’ABA), DUK WANDA YAYI SALLAH A CIKIN MASALLACIN KA’ABA NA MAKKA YANA DA LADA DUBU DARI (100,000). Ibn Maja:1406.
Shugaban ya ce Amma abin takaici duk da wannan Falala da ke tare a wannan masallaci, za ka ga wasu sun maida bakin harabarsa wurin hiran Duniya, kamar bakin wani otel mai inuwa a bakin Masallacin, wanda ake kira Daruttauhid, za ka ga mutane daba-daba ana tattauna matsalar duniya, Wasu na hirar ’yan kwallo, wasu na hirar siyasa, wasu na kulla kasuwa, wasu ma suna gidajjen su suna sharar barci a nan cikin garin Makkah, in ka musu magana sai su ce maka ai duk garin Makkah Harami ne, sai su kafa maka hujja da wannan ayar “Tsarki ya tabbata ga wanda ya tafiyar dare da bawanSa daga masallaci mai alfama (Ka’aba) zuwa masallaci mafi nisa (Baitul Mukaddas) Surah Isra’i 1)).
Masana lissafi sun yi lissafin cewa duk wanda ya yi Sallah a masallacin Ka’aba koda raka’a biyu ne da kai wanda ba a wannan Masallacin ka yi ba, sai ka yi Shekaru kusan 64 kana Sallah Kafin ka samu ladar da ya samu, ina kuma in ya samu Sallolin farillai guda biyar? Ina kuma ga yayi ta nafilfili? Ina ma da karatun Alkur’ani mai girma ka yi ta yi ba tare da gajiyawa ba? ina ma da azkar ka yi ta zabgawa da neman rahamar ubangiji? Lallai da hakan shi ne mafi alheri a gareka a wannan masallaci mai daraja.
Maniyyata a guji zama a bakin inuwa ana ta bata lokaci ba tare da yin abin da aka je yi ba, a dage da ibada, dubban mutane suna son zuwa wannan wuri Allah bai ba su dama ba, kai da ka samu dama kada ka yi wasa da damar ka.
Da fatar ni ma da nake wannan rubutu ba za ku manta da ni ba a wajen addu’oin ku na alkhairi.
Muna addu’ar Allah ya kai duk wanda bai je ba ya je ya yi Sallah a wannan masallaci mai tarin daraja, wanda yaje kuma Allah ya maida shi.
Ina rufewa da Hadisin Manzan Allah (SAW), inda ya ce “Duk wanda ya yi Hajji, be yi rafasu ba – wato bai yi Jima’i a cikinsa ba- kuma bai yi fasikanci ba –wato sabon Allah- zai koma mara laifi kamar ranar da mahaifiyarsa ta haife shi” Bukhari da Muslim.
’Yin aikin Umurah zuwa Umurah ana kankare zunubbai da ke tsakaninsu, shi ko aikin Hajji karbabbe baya da sakamako se Aljanna.) Bukhari da muslim”.
“yayin da aka tambaye shi game da mafificin ayyuka, sai ya ce “ Imani da Allah da manzonSa” aka ce sai me kuma? Ya ce “sai jihadi don daukaka kalmar Allah” aka ce sai me kuma? Ya ce” sai aikin Hajji karbabbe”. Bukhari da Muslim”.
Muna addu’ar Allah ya karbi ayyukan Hajjin mu.Wannan rana ita ce shugabar ranakun Shekara, kuma mafificiya cikin yini, Allah yana saukowa kusa da bayinSa yana bada garabasar (Bonus) din Karbar addu’a, shi ya sa Annabi (SAW) ya ce: “Mafificiyar addua’a, addu’ar ranar Arfa”. Ina Mana tuni da mu sanya kasarmu cikin addu’an Allah ya yaye mana musibar da ta addabemu, tare da rokon zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasar mu da sauran kasashen Musulmi.
Sheikh Abdullahi Bala Lau.
(National Chairman Jibwis Nigeria).
[email protected]

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50

Jami’an Sibil Difens sun kashe mayaƙan Boko Haram 50

Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 30 a Borno

DAGA LARABA: Hanyoyin Dawo Da Martabar Karatun Tsangaya