Gwabzawa tsakanin Hezbollah da Isra’ila na ta’azzara fargabar bazuwar rikici

Jiragen yakin Isra’ilar sun yi luguden wuta mafi muni tun da ƙasar da kungiyar Hezbollar ta Lebanon suka fara gwabzawa

Gwabzawa tsakanin Hezbollah da Isra’ila na ta’azzara fargabar bazuwar rikici

An ci gaba da mummunan musayar wuta tsakanin Isra’ila da Hezbollah a ranar Lahadi, inda jiragen yakin Isra’ilar suka yi luguden wuta mafi muni tun da ƙasar da kungiyar ta Lebanon suka fara gwabzawa, kusan shekara guda da ta wuce, a yayin da Hezbollah ɗin ta harba ɗimbim rokoki cikin Arewacin Isra’ila.

Ministan tsaron Isra’ila, Yoav Gallant, ya ce za a ci gaba da hare-hare har sai ya kasance babu  hatsari idan mutanen da aka kwashe daga yankin za su iya komawa.

Runduna Sojin Isra’ila ta fara sanar da kakkabo makaman roka kusan guda 100 da mayakan Hezbollah masu kusanci da Iran suka cilla cikin kasar.

Rikicin ya kazanta ne bayan wani mumunan harin da Isra’ila ta kai a tsakiyar birnin Beirut a ranar juma’a da ta gabata, inda ta kashe mayakan Hezbollah 37  ciki har da Kwamnadan Rundunar al-Radwani, wadda ta kitsa  kai harin rana 7 ga watan Oktoba a Isra’ila.

Ta cikin wata sanarwa da ta fitar , Runduna Sojin Isra’ila ta ce harin ya farmaki maboyan mayakan Hamas akalla 180 ba tare da yin karin bayani kan wadanne daga cikin su ne ba.

A nata bangare runduna mayakan Hezbollah, ta harba makaman roka akalla guda 90 a arewacin Isra’ila daga Lebanon, harin da ta ce ta kai shi ne kan wasu cibiyoyin Sojin Isra’ila biyu a matsayin martani kan hare haren makiya.

Sojin sama sun yi kuskuren kashe mutum 16 a Zamfara

Rikicin Masarautar Kano: Tsagin Aminu Ado Bayero zai ɗaukaka ƙara

Yadda Jimmy Carter ya ceto rayuwata – Obasanjo

Sojoji sun lalata sansanin Bello Turji, sun kuɓutar da mutum 7