Gwagwarmayar Ahmadu Haruna Zago, Bakaniken Jam’iyya

Baya ga siyasa, Alhaji Ahmadu Haruna Zago, sanannen ɗan kasuwar canji ne, a kasuwar canjin kuɗi ta Wafa da ke Kano

Gwagwarmayar Ahmadu Haruna Zago, Bakaniken Jam’iyya

Alhaji Ahmad Haruna Zago da aka fi sani da Ɗan zago, gogaggen ɗan siyasa ne da ya fara siyasa tun a Jamhuriya ta biyu.

Bayan dawowar Najeriya mulkin farar hula a shekarar 1999, ya shiga Jam’iyyar APP, inda ya kasance na gaba-gaba a tafiyar siyasar jam’iyyar a Kano da ma kasa baki ɗaya.

Yana daga cikin waɗanda suka jawo Muhammadu Buhari shiga cikin harkokin siyasa.

2003.

Gabanin zaɓen 2003, Alhaji Ahmadu Haruna zago ya taka rawa a tunja-tunjar da ta biyo bayan zaɓen fitar da gwani na Jam’iyyar APP, da ta kai ga karɓe takarar gwamna daga hannun tsohon shugaban jam’iyyar, Ibrahim Al’amin Little, aka bai wa Malam Ibrahim Shekarau.

2007

Sai dai tun ba a je ko’ina ba, suka samu saɓani da Malam Ibrahim Shekarau kan shugabancin jam’iyyar, wadda da ta koma ANPP.

Hakan ta sa duk da bai fita daga jam’iyyar ba, Ɗan Zago, da ƙungiyarsa ta “Zago Aƙida” ba su goyi bayan tazarcen Shekarau ba a zaɓen 2007.

Sannan kuma, kusancin Ɗan Zago da Buhari ta sa Buhari bai je Kano yi wa Shekarau kamfe ba.

2011

Gabanin zaɓen 2011, Ahmadu Haruna zago, ya bi tawagar Buhari wajen ficewa daga ANPP tare da kafa sabuwar jam’iyya ta CPC.

Shi ne ya shugabanci jam’iyyar a mataki na riko.

Sai dai daga baya, an yi ta samun rikicin shugabancin jam’iyya tsakaninsa da wasu ’yan CPC a Kano.

2015

Jam’iyyun ANPP, CPC, ACN, sun haɗe da ’yan G-5 na Jam’iyyar PDP, irin su Injiniya Rabi’u Musa Kwankwaso, wajen kafa sabuwar jam’iyyar APC.

A wannan lokaci ne, Ɗan Zago, karon farko ya bar Buhari, ya goyi da bayan Kwankwaso a zaɓen cikin gida na takarar shugabancin ƙasa.

Hakan ta sa duk da ɗawainiyar tallata Buhari da yanyi na tsawon shekaru, bai amfana da gwamnatinsa ba.

2019

A gwamnatin Dakta Abdullahi Umar Ganduje, Ahmadu Zago ya riƙe muƙamin mai bai wa gwamna shawara na musamman kan harkokin noma.

2023

Bayan ƙarewar wa’adin shugaban jam’iyyar APC reshen Jihar Kano, Alh. Abdullahi Abbas, Ɗan zago, ya nuna sha’awarsa ta fitowa takara.

Sai dai zaɓen ya bar baya da ƙura, domin sai da aka yi ta fama a kotu, yau a ce Ɗan Zago ne, gobe a ce Abdullahi Abbas ne. Abin da ya raba kan jam’iyyar APC biyu a Kano.

Wasu jiga-jigan jam’iyyar kamar Barau I. Jibril da Malam Ibrahim Shekarau da Sha’aban Ibrahim Sharada, su ne a ɓangaren Ahmadu Zago, yayin da gwamnatin Ganduje ta ce Abdullahi Abbas, shi ne ya sake cin zaɓen shugabancin jam’iyyar APC a karo na biyu.

Duk da Ahmadu Zango bai bar jam’iyyar APC ba, shi da jama’ar sa ta “Zago Aƙida” sun sha fitowa rediyo, suna barranta kansu da duk wata tafiyar siyasa da take da alaƙa da Ganduje.

Bayan lashe zaɓe da Abba Kabir Yusuf ya yi, ya baiwa Alhaji Ahmadu Haruna Zago, shugabancin hukumar kwashe shara ta Jihar Kano (REMASAB), matsayin da yake riƙe da shi har zuwa ƙarshen rayuwarsa.

Ya mutu ya bar ’ya’ya da jikoki da dama.

Baya ga siyasa, Alhaji Ahmadu Haruna Zago, sanannen ɗan kasuwar canji ne, a kasuwar canjin kuɗi ta Wafa da ke Kano.

An tara Naira 16 a taron ƙaddamar da littafin IBB

Ba ni da hannu a kisan Dele Giwa — Janar Babangida

NAJERIYA A YAU: Dalilan Da Ba Za Mu Sauke Farashin Burodi Ba —’Yan kasuwa

Ɗaliba ta rasu yayin da gini ya rufta a GGTC Potiskum