Gwagwarmayar Rayuwa: Waiwaye adon tafiya (1)

ABDULHADI AHMAD BAWA (08036674500), shi ne Mataimaki na Musamman ga Gwamnan Jihar Katsina, Alhaji Aminu Bello Masari a bangaren kafofin sadarwar zamani (Soshiyal-Midiya). dan siyasa ne da ya kwana biyu yana gwagwarmayar siyasa. A wannan makon, ya waiwaya baya ya zayyano fadi-tashin da ya sha tun daga jiya zuwa yau: A ranar wata Lahadi a […]

Gwagwarmayar Rayuwa: Waiwaye adon tafiya (1)
Gwagwarmayar Rayuwa: Waiwaye adon tafiya (1)

ABDULHADI AHMAD BAWA (08036674500), shi ne Mataimaki na Musamman ga Gwamnan Jihar Katsina, Alhaji Aminu Bello Masari a bangaren kafofin sadarwar zamani (Soshiyal-Midiya). dan siyasa ne da ya kwana biyu yana gwagwarmayar siyasa. A wannan makon, ya waiwaya baya ya zayyano fadi-tashin da ya sha tun daga jiya zuwa yau:

A ranar wata Lahadi a wata shida na karshen shekarar 2013, ni da wadansu abokan gwagwarmaya muka kai wa Mai girma tsohon Shugaban Majalisar Wakilai, Alhaji Aminu Bello Masari ziyara a gidansa da ke Kaduna. A lokacin shi ne Mataimakin Shugaban sabuwar jam’iyyarmu ta APC.

Kafin in ci gaba, mai karatu ina so ka san cewa ban taba haduwa gaba-da-gaba da Dallatun Katsina ba, amma na san shi, muna haduwa a wurare daban-daban, amma dai wannan ita ce haduwata ta farko da shi.

Dalilin zuwanmu shi ne mu nuna masa damuwarmu a kan yadda hidimar jam’iyyar ke neman suɓucewa daga inda ya kamata. Kuma mun tattauna na tsawon lokaci da shi kuma mun fahimci juna, duk kuwa da cewa abin da muka zo da shi ya sha bamban da matsayarsa, saboda ya gamsar da mu da abin da Bature ke ce wa “Superior Argument,” wato gamsasshen bayani.

Bayan wannan, ba mu sake haduwa da shi ba, sai a ranar wata Asabar da wani tsohon wakili a Majalisar Tarayya ya bukaci in kai shi gidan Dallatu a nan Katsina. A lokacin masu son takarar Gwamna duk sun fito ana ta hidimar neman mutane. Mun tarar da Dallatun yana ganawa da masu ƙurƙura da kuma wadansu dalibai. Bayan da ya sallame su, muka isa aka gaggaisa cikin karamci; daga bisani na ba su wuri suka gana.

To, daga wannan rana ba mu sake haduwa ba, sai bayan da aka gama zaben fitar da gwani kuma Allah Ya sa Alhaji Aminu Bello Masari ya dauki tuta.

Ni kaina na nemi kujerar Majalisar Dokoki ta Jihar Katsina a wancan lokaci amma Allah bai kaddara ba, kuma na yi hulda da mutane da dama, wanda hakan ya kara mini ilimi kwarai kan al’amuran siyasa da na hulda da jama’a.

Abubuwan da suka faru kafin da kuma lokacin zaben fitar da gwani sai idan Allah Ya ara mini lokaci zan bayyana su dalla-dalla a wani rubutu da zan fara ba da jimawa ba kan abin da ya shafi rayuwata.

Amma dai a takaice, bayan kammala zabubbukan fitar da gwani, sai mai gidana kuma aminina, Dokta Lawal Usman Bagiwa ya gaya mini cewa ya yi magana da Dallatu kan a shigo da ni cikin ayyukan ofishin yakin neman zabe na Rt Hon. Aminu Bello Masari (RESTORATION PROJECT) domin akwai gudunmawa da rawar da zan iya takawa. Bayan wannan kuma sai yayyena a gwagwarmaya, Isa Ahmed da Maiwada dammalam su ma suka kira ni muka tattauna, duk a kan hidimar tafiyar Dallatu. Na kuma amsa cewa zan yi wannan hidima cikin gaskiya da amana.

A wannan ofishi na yaƙin neman zaɓe an saka ni a kwamitin da aka ɗora wa alhakin gudanar da tsare-tsare da nazari (Planning and Research). Kuma alhamdulillah mun yi aiki bakin iyawarmu cikin aminci da amana.

A wannan kwamiti, muka fito da shawarar yin ’yan sharar hanya, wadanda za su fara isa karamar hukuma da jirgin yakin neman zaben zai je domin a samu duk bayanin da ake bukata. Haka kuma a tuntuɓi duk waɗanda suka shiga zaɓen fitar da gwani da ba su samu nasara ba, domin a ba juna haƙuri kuma a tafi tare domin samun nasara. Mun kuma yi aikin tantancewa da buga sunayen masu kula da akwatunan zabe (mutum 4902, idan ban manta lissafin ba).

Dukan wadannan ayyuka, mun yi su kuma mun gama lafiya duk da ƙalubalen da muka riƙa fuskanta, musamman ma na tsaro.

Za mu ci gaba