Gwagwarmayar rayuwa: Waiwaye adon tafiya (2)

ABDULHADI AHMAD BAWA (08036674500), shi ne Mataimaki na Musamman ga Gwamnan Jihar Katsina, Alhaji Aminu Bello Masari a bangaren Soshiyal-Midiya. dan siyasa ne da ya kwana biyu yana gwagwarmayar siyasa. A makon jiya, ya waiwaya baya ne ya zayyano irin fadi-tashin da ya sha tun daga jiya zuwa yau. Ga kashi na biyu:   Bayan […]

Gwagwarmayar rayuwa: Waiwaye adon tafiya (2)
Gwagwarmayar rayuwa: Waiwaye adon tafiya (2)

ABDULHADI AHMAD BAWA (08036674500), shi ne Mataimaki na Musamman ga Gwamnan Jihar Katsina, Alhaji Aminu Bello Masari a bangaren Soshiyal-Midiya. dan siyasa ne da ya kwana biyu yana gwagwarmayar siyasa. A makon jiya, ya waiwaya baya ne ya zayyano irin fadi-tashin da ya sha tun daga jiya zuwa yau. Ga kashi na biyu:

 

Bayan kammala zabe tare da samun gagarumar nasara ga jam’iyyarmu ta APC, sai kuma muka duƙufa wajen bin diddigin alƙaluman zaɓen Gwamna a kaf ɗin ƙananan hukumomin da suke jihar nan.

Wannan ƙwaƙƙwafi da bin diddigi mun yi shi ne musamman don mu gano inda muke da buƙatar yin gyare-gyare saboda yadda za a tafiyar da ayyuka idan an kafa gwamnati da kuma ita kanta hidimar siyasar.

Babban Daraktan Kamfen kuma Shugabanmu a Restoration Project, Alhaji Muntari Lawal ya danƙa mini cikakken sakamakon zaɓen tare da umarta ta in natsu wuri guda in yi wancan aiki da na ambata a sama. Cikin iko da yardar Allah na kammala shi a kasa da sa’a ashirin da huɗu.

A kowace ƙaramar hukuma mun fitar da yawan waɗanda suka yi rajista da hukumar zaɓe, muka fitar da yawan waɗanda suka jefa ƙuri’a, muka fitar da ƙuri’ar da ta baci da ta sauran ’yan takara. Sannan muka fitar da kason da Dallatun Katsina ya samu cikin kashi ɗari na halattattun ƙuri’un da aka kaɗa a zaɓen. Wannan jaddawali shi ya fito mana da yadda hajar APC/BUHARI/DALLATU ta yi kasuwa a wannan jiha.

Kamar yadda na yi bayani a baya, kwamitinmu shi ke kula da tsare-tsare da nazari, wannan ya sanya muka duƙufa wajen tattara alƙaluma da bayanan alƙawura da kuma buƙatun al’umma da suka yi musayar hannu tsakanin al’umma da Dallatun Katsina.

Domin samun nasarar wannan aiki, mun yi amfani da jawaban da aka gabatar wajen yaƙin neman zaɓe, na fage da na kafafen watsa labarai. Sannan muka haɗa da amsar bayanai daga masu kula da hidimar Dallatu a matakin ƙananan hukumomi.

Bayan kammala tattara waɗannan bayanai, sai aka ƙara ɗora mini alhakin buga su a kwamfuta. Wannan shi ne babban abin alfaharina na farko a wannan tafiya, domin da hannuna na buga su daki-daki. Kowace ƙaramar hukuma da nata, sannan na fitar a jimlatance ɓangare-ɓangare. Abin nufi shi ne, aka fitar da ayyukan da suka shafi ilimi daban, lafiya daban, ruwan sha da sauransu.

Wannan kundi na nan kammale, kuma da shi muke lissafin abubuwan da aka aiwatar da wadanda suke layi.

Wannan ayyuka biyu sun sa mini natsuwar cewa haƙiƙa Dallatu ya shirya wa yi wa al’ummar Jihar Katsina adalci gwargwadon iko. Kuma ganin yadda ya ba abubuwan duk da aka sa gaba muhimmanci tare da tunkarar duk ƙalubalen da muke fuskanta cikin natsuwa, fahimta da kwanciyar hankali, kana ga iya tafiyar da al’umma ya sa na fahimci duk wanda zai yi aiki da shi, to zai ƙaru da ilimi daban-daban, sai dai idan bai so ba, ko kuma yana da ƙarancin fahimta.

Kaf wannan, bai sa ni tunani ko ƙoƙarin nema ko a ba ni muƙami ba, domin ban kalli kaina a cikin sahun wadanda za su yi haka ba; ni da ma babban burina mu kafa gwamnati, domin kawo gyara da saita al’amurra, don kyautata rayuwar al’umma a ƙarƙashin jagorancin Baba Buhari kuma al’umma su natsu kuma su gane cewa ƙuri’arsu ita ce matakin hawa kowane muƙami.

Bayan an yi rantsuwa an kafa gwamnati sai muka ci gaba da hidimominmu na yau da kullum tare da ci gaba da yaɗa manufofi da fahimtar da al’umma yadda aka samu gwamnati a durƙushe kuma kanannaɗe da matsalolin da suke tattare da ƙalubale da dama.

Muna cikin waɗannan hidimomin, Allah da ikonSa sai Mai girma Gwamna Aminu Bello Masari ya naɗa Maiwada dammalam a matsayin Babban Mataimaki na Musamman (SSA) a al’amuran da suka shafi Soshiyal Midiya.

Wannan naɗi shi ya kafa harsashin ɗaukakar wannan kafa ta sadarwa. Ba tare da wani jinkiri ba, Maiwada ya duƙufa wajen ganin ya yi wa wannan naɗi adalci ta wajen bayyanawa tare da wayar da kan al’umma a kan inda gwamnati ta sa gaba da kuma abubuwan da take yi ko take ciki.

Ana nan kuma sai Allah Ya sa Ministan Harkokin Matasa da Wasanni, Mista Solomon Dalung ya naɗa Maiwada dammalam a matsayin Mataimaki na Musamman.

Yau zan faɗi abin da ba kowa ya sani ba, kuma yana daga cikin dalilan da ya sa nake wannan dogon rubutun, tare da fatar mai karatu zai ƙara hakuri.

Wannan sabon matsayi da Maiwada ya samu ya ba da damar Gwamna Masari ya cike gurbin da zai bari. Allah Shi ke shaida, ban je wajen kowa ba kuma ban yi wa kowa magana ba, amma na roƙi Allah Ya ba ni wannan matsayi domin ina ganin kamar zan iya riƙe shi. Allah kuma Maji roƙon bawa, ina zaune gida Maiwada ya kira ni da bayanin cewa “Mai girma (Gwamna) ya ce ka ba da takardun bayaninka zai naɗa ka SA Social Media.” Da haka Allah cikin hikima da isarSa Ya kawo ni nan.

Abin da nake so mai karatu ya fahimta a nan, duk hidimar da muka yi a Restoration Project, muna karkashin jagorancin DG Alhaji Muntari Lawal, saboda haka ba safai muke aiki kai-tsaye da Dallatu ba, kuma da ma tun farko a bayanina, za a fahimci cewa babu wani sabo sosai tsakanina da shi. Amma cikin ikon Allah Ya amince da ba ni wannan matsayi ba tare da ya kira ni ba, ko ya sa wani ya kira ni ba, domin tantancewa. Bayanin da ya samu wurin Maiwada kadai ya ishe shi, kuma ya tsaya kansa.

Wannan ya kara nuna mini karamcin Dallatu da yadda yake sa aminci da yarda a cikin huldarsa da jama’a. Yardar ta sa ya amince da bayanin Maiwada, karamcin da amincin ya sa shi ya ba ni wannan matsayi. Na kama wannan aiki da zuciya ɗaya tare da karanta wa kaina cewa haƙuri na cikin matakan nasara.

Za a kammala makon gobe