Gwajin jini da na HIV kafin aure ya zama dole a Kano

Majalisar Dokokin Jihar Kano ta amince da dokar tilasta yin gwajin cutar HIV, ciwon hanta da na sikila ga masu shirin yin aure kafin a daura

Gwajin jini da na HIV kafin aure ya zama dole a Kano

Ana ta cece-kuce gameda wanda ya kamata ya fara gaida wani tsakanin miji da mata

Majalisar Dokokin Jihar Kano ta amince da dokar tilasta yin gwajin cutar HIV, ciwon hanta da na sikila ga masu shirin yin aure.

Shugaban majalisar, Ismail Falgore ne ya bayyana hakan a zaman majalisar na ranar Litinin.

Bayan zama biyun farko kan ƙuɗurin ne suka amince da shi a karatu na 3, wanda mataimakin magatakardar majalisar, Nasiru Magaji ya karanta.

Jim kadan bayan amincewa da kudirin dokar, shugaban masu rinjaye na majalisar, Lawan Hussaini mai wakiltar Dala, ya bayyana cewa: “Yanzu duk mai niyyar yin aure sai ya fara mika kansa domin a duba lafiyarsa.”

Ya ce an yi la’akari wajen yin dokar ne bayan an bi tsarin dokoki daban-daban wajen gabatar da kudurin doka a jihar.

Honarabul Lawan Hussaini ya ci gaba da cewa an yi dokar ne saboda jihar na fama da matsalolin lafiya da suka hada da HIV, saboda mutane suna yin aure ba tare da an tantance lafiyarsu ba.

Ya ce idan aka sanya wa dokar hannu, za ta ceci rayuka da dama tare da dakile yaduwar cututtuka masu barazana ga rayuwa.

“Kudirin dokar zai kare lafiyar ’yan kasa ta hanyar tilasta gwaje-gwaje kafin a yi aure domin dakile yaduwar cututtuka kamar ciwon hanta, HIV da sankarar jini,” kamar yadda Kamfanin Dillacin Labaran Najeriya (NAN) ya ruwaito.

A Najeriya dai dama masallatai da dama sun ɗauki tsarin gabatar da takardar gwajin lafiya kafin aure a matsayin ƙa’idojin ɗaura aure.

Duk da dai har yanzu ana samun masu ganin yin wannan gwaji ya saɓa wa al’ada da addini, yawancin jama’a sun  aminta da tsarin.