Gwajin Nukiliyar Koriya ta Arewa ya janyo ‘ruftawar kasa’
Da alama gwajin Nukuliyar da Koriya ta Arewa ta yi ya janyo ruftawar kasa a fadin yankin bayan da aka samu hotunan tauraron dan Adam na yankin da abin ya faru. Gwajin na ranar Lahadi ya auku ne a karkashin kasa da ke yankin tsaunin Pungye-ri. Gidan rediyon BBC, ya ce kungiyar masu nazari, 38 […]

Da alama gwajin Nukuliyar da Koriya ta Arewa ta yi ya janyo ruftawar kasa a fadin yankin bayan da aka samu hotunan tauraron dan Adam na yankin da abin ya faru.
Gwajin na ranar Lahadi ya auku ne a karkashin kasa da ke yankin tsaunin Pungye-ri.
Gidan rediyon BBC, ya ce kungiyar masu nazari, 38 North sun wallafa hotunan da ke nuna yadda gwajin ya “janyo barna mai yawa da kuma fadi” fiye da yadda aka zata a baya.
Gwajin ya janyo wata gagarumar girgizar kasa mai karfin maki 6.3 a ma’aunin Richter, wadda har aka ji ta a makwabciyar kasar China.
Koriya ta Arewa ta gudanar da gwaje-gwaje shida kawo yanzu, duk a yankin na Punggye-ri wanda yake da ramukan da aka haka a karkashin jerin tsaunuka.
kungiyar 38 North ta ce wadannan sababbin hotuna da aka dauke su kwana guda bayan gwajin na ranar Lahadi sun nuna ruftawar kasa a yankuna masu yawa a dalilin girgizar kasar da ta biyo bayan gwajin.
Yanayin mai suna “lofting” (ruftawa) kan auku ne idan girgiza mai karfi ta sanya kasa ta tashi sama kuma ta dawo wurin da take a da.
Ruftawar ta auku ne a kusa da tsaunin Mantap, wanda shi ne tsauni mafi tsawo a yankin da aka yi gwajin. “Sun zarce illar da aka zata a baya, kuma abin ya bazu fiye da na sauran gwaje-gwajen da Koriya ta Arewa ta aiwatar a baya,” inji masu binciken. Amma sun kara da cewa gwajin bai janyo rugujewar tsaunin ba.
Amma wadansu masu bincike na da ra’ayin cewa wani ramin da ke karkashin dutse a yankin ya rufta a sanadiyyar gwajin na Punggye-ri.
Ana zaton bam din da aka gwada ranar Lahadi yana da karfin da ya kai tan 50 zuwa 150. Bam mai karfin ton 50 ya yi ukun wanda Amurka ta yi amfani da shi a kan birnin Hiroshima na Japan a lokacin Yakin Duniya na Biyu a 1945.
Wannan lamarin yana janyo rarrabuwar kawunan masana dangane da tasirin yawan gwaje-gwajen.