Gwajin riga-kafin COVID-19 ya shiga mataki na biyu

Maganin riga-kafin COVID-19 da Cibiyar Kimiyyar Tsirrai ta Kwalejin Kimiyyar Kiwon Lafiya a Kasar China ta samar ya shiga matakin gwaji na biyu a kasar. Kafar yada labarai ta kimiyya da fasaha ta (Science and Technology Daily Report) ta sanar da haka a ranar Asabar 20, ga watan Yuni. Gwajin da aka yi a matakin […]

Gwajin riga-kafin COVID-19 ya shiga mataki na biyu

Jami’in kiwon lafiya dauke da kwalbar samfurin gwajin cuta Coronavirus

Maganin riga-kafin COVID-19 da Cibiyar Kimiyyar Tsirrai ta Kwalejin Kimiyyar Kiwon Lafiya a Kasar China ta samar ya shiga matakin gwaji na biyu a kasar.

Kafar yada labarai ta kimiyya da fasaha ta (Science and Technology Daily Report) ta sanar da haka a ranar Asabar 20, ga watan Yuni.

Gwajin da aka yi a matakin na biyu a yankin Kudu maso Yammacin Yunnan, ya gano tasirin maganin riga-kafin wajen bunkasa garkuwar jiki tare da rashin illarsa a cikin dan Adam.

Zuwa yanzu dai maganin riga-kafin COVID-19 biyar ne aka amince a yi gwajinsu a kasar China wato  kaso 40 bisa 100 na maganin riga-kafin cutar a fadin duniya, a cewar  ma’aikatar kimiyya da fasaha ta kasar.

Ba mu yanke hukunci kan ƙudirin harajin Tinubu ba — Abbas

Masu garkuwa da mutane na neman N10m kan manoma 6 a Taraba

Hotunan Gobarar Kasuwar Laranto da ke Jos

Kasuwar Laranto da ke Jos ta yi gobara