Gwaman Kaduna ya gargadi maso son haddasa rikicin addini a jihar

Ranar Talatar da ta gabata ce Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai ya gargadi masu neman janyo rikicin addini a jihar da cewa duk wanda aka kama da neman janyo irin wannan rikici zai dandana kudarsa. Wannan sanarwa ta gwamnan ta fito ne bayan wani taro da majalisar tsaro ta jihar ta yi a kan […]

Gwaman Kaduna ya gargadi maso son haddasa rikicin addini a jihar
Gwaman Kaduna ya gargadi maso son haddasa rikicin addini a jihar

Ranar Talatar da ta gabata ce Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai ya gargadi masu neman janyo rikicin addini a jihar da cewa duk wanda aka kama da neman janyo irin wannan rikici zai dandana kudarsa.

Wannan sanarwa ta gwamnan ta fito ne bayan wani taro da majalisar tsaro ta jihar ta yi a kan wani lamari da ya auku a unguwar Kawo, inda ya nemi janyo rikicin addini a jihar.
Wata sanarwa mai dauke da sa hannun Kakakin gwamnan jihar, Samuel Aruwan, ya ce gwamnan ya kuma gargadi jama’a da su guji daukar doka a hannunsu. Ya ce duk wanda ya dauki hukunci a hanunsa a kan dan uwansa, za a hukunta shi a kotu.
“Majalisar Tsaro ta Gwamnatin Jihar Kaduna za ta tabbatar da kare rayuka da dukiyoyin jama’ar jihar. Za mu dau matakan da suka dace a kan duk wani mutum komai matsayinsa da muka samu da neman tada rikicin addini ko na kabilanci ko na siyasa ko kuma duk wani irin rikici a jihar,” inji shi.
Har ila yau, gwamnatin ta kuma sake jaddada cewa dokar hana yin goyo a kan babur na nan daram a jihar. Ya ce tuni an umurci jami’an tsaro da su tabbatar sun tilasta jama’a bin wannan doka tare da hukunta duk wanda aka kama da karya ta.
Majalisar tsaron ta kuma yaba wa jama’a a kan bin doka da oda da suke yi a jihar tare da goyon baya da suke ba jami’an tsaro.
“Muna kuma kira ga jama’a da su rika sanya ido tare da ba jami’an tsaro rahoton mutane da ba su yarda da su ba cikin jama’a,” inji shi.