Gwammoni na kashe 80% na kudaden shigar jihohinsu wajen biyan bashi

Biyan bashin ya cinye kashi 80.7% na kudaden shigar jihohinsu

Gwammoni na kashe 80% na kudaden shigar jihohinsu wajen biyan bashi

Biyan bashin da gwamnoni suka ciyo ya cinye kashi 80.7 na kudaden shigar jihohi 29 a watanni shida na farkon shekarar 2024 da muke ciki.

Gwamnonin jihohin sun ciyo bashin Naira biliyan 446.26, duk kuwa da karuwar kudaden da jihohin suke samu daga Asusun Tarayya (FAAC) da kashi 40% a shekara guda da ta gabata.

Alkaluma sun nuna cewa a halin da ake ciki abin da wasu jihohi tara suke kashewa wajen biyan bashi ya zarce kudaden shigar da suke tarawa a cikin gida.

Wasu ggwamnoni 22 sun kashe Naira biliyan 251.79 wajen biyan bashin da gwamnatocin da suka gada suka bari, daga watan yulin 2023 zuwa Maris 2024, bayan sun karbi mulki.

Ana kuma abin jihohi jimillar bashin Naira tiriliyan 2.1 a cikin gida da kuma Dala biliyan 1.9 a kasashen waje da gwamnonin suka gada.

Shirin Taurin Bashi

Hakan ta sa jihohin Ekiti, Kuros Riba da Ogun neman daina da biyan basukan kasar waje na Dala miliyan 501 da suka ciyo, sakamakon  tashin Dala, amma FAAC ya ki amincewa.

Jihohin sun yi haka ne da nufin rage yawan nauyin biyan basukan, wadanda kwararru suka ce na kawo cikas ga ayyuka a fannin ilimi, kiwon lafiya da sauran bangarorin domin bunkasa tattalin arziki da cigaban al’umma.

Nauyin Bashi

Alkaluma sun nuna cewa jihohi tara da ke kashe fiye da kudaden shigar da suke tarawa a tsawon lokacin su ne: Adamawa, Bauchi, Gombe, Imo, Kano, Kogi, Filato, Taraba, da Yobe.

Su Akwa-Ibom, Borno, Kuros Riba, Edo, Katsina, da Neja, suna kashe kashi 60 zuwa 80 na kudaden shigar da suke tarawa wajen biyan basuka.

Abia, Anambra, Bayelsa, Delta, Ebonyi, Ekiti, Jigawa, Enugu, Kebbi, Kwara, Ondo, Osun, Zamfara da Oyo kuma, abin da suke kashewa na kudaden shigar da suke tarawa wajen biyan bashi ya kai 13 zuwa 58 cikin 100.

Ba a samu alkaluman jihohin Binuwe, Nasarawa, Ogun, Ribas, Sokkwato da Kaduna ba.

Amnm Jihar Legas na da kudaden shiga na cikin gida Naira biliyan 603.71, amma bashin biliyan N201.49 ake bin ta.

An samo wadannan alkaluma ne daga rahoton aiwatar da kasafin kuɗi a shafukan intanet na jiohin da kuma shafin Open Nigeria States, wadda ma’ajiyar bayanan kasafin kuɗin gwamnati ce.

Rahoton aiwatar da kasafin, ana shirya shi ne bayan duk wata uku, sannan a ba da shi ne a cikin makonni huɗu watan ƙarshen watanni ukun.

Cikas ga Ayyukan Cigaba

Wannan halin da ake ciki ya sa akasarin kudaden shiga da jihohi suke tarawa domin gudanar da muhimman ayyukan cigaba suke tafiya wajen biyan bashi.

Wannan babbar matsala ce gare su wajen tafiyar da basukan da suka gada daga gwamnatocin baya da kuma biyan bukatun al’ummarsu.

Halin da ake ciki

’Yan Najeriya dai sun yi fatan cewa da karin kaso 40% na abin da jihohinsu ke samu daga FAAC, ya kamata a ce gwamnoni sun samu fiye da abin da suke bukata wajen sauke nauyin al’umma da ya rataya a wuyansu.

A 2023 gwamnonin suka sami mafi yawan kason FAAC a cikin shekaru bakwai, sakamakon cire tallafin mai da sake fasalin kudin gwamnati da mai ci ta kaddamar.

Rahotanni sun ce sauye-sauyen ne suka haifar da karuwar kashi 40 na kudaden FAAC, lamarin da

Masana na ganin kamata ya yi karuwar kudaden FAAC ta rage wa gwamnatocin jihohi sha’awar karbar bashi.

Amma maimakon haka, gwamnatocin jihohi sai kashe kaso mai tsoka suke yi wajen biyan basussuka da kuma karbo wasu.

Nauyin da ke kan jihohi

A halin da ake ciki, ana bin gwamnonin jihohi bashin da suka gada na Naira tiriliyan 2.1 na cikin gida da kuma Dala biliyan 1.9 na kasashen waje.

Hakazalika akwai gagarumin aiki a gabansu na inganta tattalin arzikin jihohinsu da kuma samar da abubuwan more rayuwa.

Sai dai alkaluma sun nuna cewa akasarin kudaden FAAC na jihohin Osun, Ondo, Kaduna, da Kuros Riba zai tafi ne wajen biyan basussuka a bana.

FAAC za ta cire biliyan biliyan 27.7, wajen biyan basukan Jihar Osun, N10.94 na Jihar Ondo, Kaduna biliyan N15.83, sai Kuros Riba biliyan 10.02.

Kaso mai yawa na kudaden FAAC na jihohi da ake biyan bashi da su, yana ƙara zama ƙalubale ga jihohi wajen gudanar da ayyukan cigaban tattalin arziki da inganta rayuwar jama’arsu.

A farkon shekarar nan ne Gwamnan Kaduna, Sanata Uba Sani ya koka bisa yadda dimbin bashin da ya gada daga gwamnatocin da suka gabace shi, ya biyan albashi a kan kari da karin karin rance a cikin watanni 9 na gwamnatinsa.

A wani taron al’umma daaga gudanar ne gwamnan ya sanar cewa ya gaji bashin Dala miliyan 587 da Naira biliyan 85, da kuma kudaden kwangolili 115.

Davido zai bai wa marayu tallafin N300m a Najeriya

Ba mu yanke hukunci kan ƙudirin harajin Tinubu ba — Abbas

Masu garkuwa da mutane na neman N10m kan manoma 6 a Taraba

Hotunan Gobarar Kasuwar Laranto da ke Jos