Gwamna Abba ya fice daga jam’iyyar NNPP

Wannan na zuwa ne biyo bayan jita-jitar sauya sheƙarsa zuwa jami’yya mai mulki, APC.

Gwamna Abba ya fice daga jam’iyyar NNPP

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya fice daga jam’iyyar NNPP, biyo bayan lokaci da aka shafe ana jita-jitar sauya sheƙarsa zuwa jami’yyar APC.

Wannan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar a ranar Juma’a.

Sanarwar ta ce gwamnan ya miƙa takardar murabus ɗinsa ga shugaban jam’iyyar NNPP na mazaɓar Diso-Chiranchi a Ƙaramar Hukumar Gwale, wanda za ta fara aiki daga ranar 25 ga watan Janairu, 2026.

“Ina rubutawa cike da godiya domin sanar da shugabancin jam’iyyar NNPP a hukumance kan shawarar da na yanke na ficewa daga jam’iyyar,” in ji gwamnan.

Gwamnan ya gode wa jam’iyyar bisa damar da ta ba shi da kuma goyon bayan da ya samu tun daga shekarar 2022.

“Ina matuƙar godiya da damar da jam’iyyar, shugabancinta da mambobinta a faɗin Jihar Kano suka ba ni,” in ji shi.

Sai dai gwamnan ya ce rikicin shugabanci da dabaibaye jam’iyyar ne silar ficewarsa.

“A ’yan kwanakin nan, jam’iyyar na fuskantar ƙalubale sakamakon rikicin shugabanci da shari’o’in da ke gaban kotu,” ya bayyana.

Ya ƙara da cewa rikicin ya raba kan mambobin jam’iyyar tare da haifar da rashin tabbas a matakin jiha da ƙasa baki ɗaya.

“Saɓani ya haddasa rarrabuwar kawuna a cikin jam’iyyar,” in ji Gwamnan.

Gwamnan ya ce ya ɗauki matakin ne bayan yin dogon nazari, domin amfanin al’ummar Jihar Kano.

“Na yanke wannan shawara ne bayan yin tunani, kuma domin amfanar da al’ummar Jihar Kano,” a cewarsa.

Sanarwar ta kuma bayyana cewa ’yan Majalisar Dokokin Jihar Kano 21, ’yan Majalisar Tarayya takwas, da shugabannin ƙananan hukumomi 44 sun fice daga NNPP tare da bin sahun gwamnan.

Sakataren NNPP na mazaɓar Diso-Chiranchi, Kabiru Zubairu, ya tabbatar da karɓar takardar murabus din gwamnan.

“Ina goyon bayan ra’ayin Mai Girma Gwamna kan rikicin da ke damun jam’iyyarmu,” in ji Zubairu.

Ya yaba wa gwamnan bisa nasarorin da ya samu a fannonin gine-gine, kiwon lafiya, ilimi da bunƙasa tattalin arziƙi.